Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta ba da sanarwar soke mukamin Farfesa da aka bai wa Ministan Sadarwa da Bunkasa Tattalin Arziki ta Fasahar Zamani, Dokta Isa Ali Pantami.
Kungiyar ta sanar da yanke hukuncin ne a ranar Litinin a wata hira da Shugabanta, Farfesa Emmanuel Osodeke ya yi da manema labarai.
- Dalilin da PDP ta lallasa APC a zaben Kananan Hukumomin Abuja
- Ko aji ban taba shiga ba, amma har jami’a na taba zuwa yin lakca – Dattijon da ya kera jirgin sama a Gombe
Ya ce, “Ba zai yiwu ka kasance minista sannan lakcara ma koyarwa a Jami’a a lokaci daya ba. Wannan ya saba da doka.
“Ba zai yiwu Pantami ya yi aiki biyu a karkashin Gwamnatin Tarayya ba. Bai cancanta ba. Bai zai yiwu a rika kiran Pantami da Farfesa ba,” a cewarsa.
Wannan sanawar dai da ASUU ta bayar na zuwa ne bayan kammala taron Majalisar Zartarwarta da ya gudana, inda ta ce bai wa Pantami mukamin ya saba wa doka.
Kazalika, ASUU ta kudurin aniyyar hukunta shugaban Jami’ar FUTo da ya bai wa Pantami mukamin na Farfesa.
An iya tun cewa, a watan Satumbar 2021 ne, rahotanni suka bulla cewa Pantami tare da wasu malamai bakwai sun samu mukamin Farfesa a Jami’ar Tarayya da ke Owerri (FUTO).
Sai dai bai wa ministan mukamin tun a wancan lokaci ya rika yamutsa hazo, inda mutane da dama suka shiga sukar mukamin da aka ba shi ganin cewar ba ya koyarwa a Jami’ar ta FUTO.
Wasu kuma na ganin ya samu mukamin ne a sakamakon a yanzu yana rike da mukamin ministan, wanda ake ganin siyasa ta taka rawa a lamarin.