Shugaban Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU), Farfesa Biodun Ogunyemi, ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta kara kaimi wajen kawo karshen ta’addancin garkuwa da mutane a fadin Najeriya.
Ogunyemi, ya bayyana haka ne a hirarsa da Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya (NAN), a garin Otta, Jihar Osun, a ranar Lahadi.
- Boko Haram: Attahiru mai fada da cikawa ne —Zulum
- Mahajjata 60,000 za a bari su yi aikin Hajji a bana
- NDLEA ta kwace hodar Ibilis ta N8bn a Legas
- Yake-yake: Tibi da Fulani sun sasanta a Taraba
’Yana daga cikin aikin gwamnati ta kare rayuka da dukiyoyin jama’arta, kuma dole ne ta sa kaimi wajen aikata hakan.
“Yana da matukar wuya a kawo karshen matsalar tsaro baki daya a tsakanin al’umma wanda rashin aiki, talauci da rashin adalci suka haifar,” a cewar Ogunyemi.
Ya kara da cewa matukar Gwamnatin Tarayya na son kawo karshen matsalar tsaro, dole ta zage damtse a yaki da ta’addanci.
Shugaban ASUU, ya ce ba daidai ba ne a rika daukar makudan kudade ana ba wa ’yan bindiga ba da sunan kudin fansa.
Sannan ya bukaci Majalisa ta tabbatar da dokar hana ba wa ’yan bindiga kudin fansa.
“Wannan ita ce mafita, sannan hanya mafi dacewa,” in ji Ogunyemi.