A yau Laraba, 28 ga watan Oktoba, ana sa ran wakilan Kungiyar Malaman Jami’o’i da na Gwamnatin Tarayya za su koma teburin sulhu domin ci gaba da tattauna wa wajen kawo karshen yajin aikin jami’o’i da ya ki ci ya ki cinye wa.
Kakakin Ma’aikatar Kwadago da Samar da Aiki, Charles Akpan ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa ta goron gayyata da ya aike wa manema labarai.
- FCE Bichi ta sanar da ranar koma wa aiki
- An hallaka mutum 5 a Katsina bisa zargin garkuwa da mutane
- #EndSARS: An cafke ‘barayi’ 238 da taraktoci 35 a Adamawa
Sanarwar Mista Akpan ta ce za a fara gudanar da zaman ne da misalin karfe 3.00 na yammacin Larabar yau a babban dakin taro na Ministan Kwadago da Samar da Aiki, Dokta Chris Ngige.
Bangarorin biyu za su ci gaba da zaman ne bayan dage zaman da su gudanar a makon jiya wanda bai haifar da da mai ido ba.
Ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin Gwamnatin Tarayya da kuma Kungiyar ASUU a sakamakon kin amincewa da sabon tsarin biyan albashin ma’aikata na bai daya IPPIS da kungiyar ta yi da kuma rashin biyan alawus din mambobinta.
Saura ababen da suka fusata kungiyar ta afka yajin aiki tsawon watanni bakwai da suka gabata sun hadar da rashin inganta jami’o’in kasar nan, zaftare albashinsu da makamantansu.
Kungiyar ASUU ta kafe a kan lallai sai Gwamnati ta amince da wani tsarin biyan albashin ma’aikatan jami’o’i na UTAS daban da wanda Gwamnatin ta kawo, wanda a halin yanzu Gwamnatin ke ci gaba da nazarin ingancinsa.