Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya (ASUU), ta ce a shirye ta ke ta janye yajin aikin da ta shafe wata bakwai tana yi muddin Gwamnatin Tarayya ta biya dukkan basussukan albashin mambobinta da aka rike.
Shugaban Kungiyar reshen Jam’iar Ibadan, Farfesa Ade Adejumo ne ya sanar da hakan ranar Laraba yayin zanta wa da manema labarai a Ibdan, babban birnin Jihar Oyo.
- Gwamnan Jigawa ya gabatar da kasafin kudi na 2021
- Yadda Najeriya za ta bunkasa kasuwanci da fasahar zamani — NITDA
- An sa ranar nadin sarautar sabon Sarkin Zazzau
Farfesa Adejumo ya ce duk da zaman sasanci da ake ci gaba da yi a tsakanin bangarorin biyu, har yanzu Gwamnatin Tarayya ta noke wajen biyan albashinsu da alawus.
Ya ce an zabi wasu daga cikin ’yan kungiyar ana biyan zaftararren albashi don kawai a rage wa kungiyar karsashi da kuzarin tattaunawa wajen neman sasanci.
Har ila yau ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin Gwamnatin Tarayya da ASUU, sakamakon kin amincewar kungiyar da sabon tsarin biyan albashin ma’aikata na bai daya (IPPIS) da kuma rashin biyan alawus din ’ya’yanta.
Saura ababen da suka fusata kungiyar ta afka yajin aiki tsawon wata bakwai da suka gabata sun hadar da rashin inganta jami’o’i, zaftare albashinsu da makamantansu.
Kungiyar ASUU ta kafe a kan cewa lallai sai Gwamnati ta amince da wani tsarin biyan albashin ma’aikatan jami’o’i na UTAS ba IPPIS ba, wanda a halin yanzu gwamnatin ke ci gaba da nazarin ingancinsa.