✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

ASUU: Saura kiris daliban jami’o’i su koma karatu – Gwamnatin Tarayya  

Ngige ya ce da alama yajin aikin ya zo karshe

Gwamnatin Tarayya ta ba da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba daliban jami’o’i za su koma makarantunsu, saboda tana ta kokarin kawo karshen yajin aikin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU).

Yanzu haka dai ASUU da ta Manyan Ma’aikatan Jami’a ta SSANU, har ma da ta wadanda ba malamai ba (NASU) na gudanar da yajin aiki kusan tsawon watanni biyar kenan.

Da yake jawabi bayan kammala taro da Majalisar Zartaswa ta kasa karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari a dakin taron da ke Fadarsa a Abuja ranar Laraba, Ministan Kwadago, Chris Ngige ya ce bisa ga dukkan alamu yajin aikin ya zo karshe.

Ministan ya kuma musanta zargin cewa Gwamnatin Tarayyar na da aniyar kirkirar wani sabon daftarin biyan kungiyoyin, inda ya ce ta ma zauna da hukumomin da ke da ruwa da tsaki ciki har da ta Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA), domin yin bayani kan nasarar da aka samu kawo yanzu, a warware matsalolin da suka haifar da yajin aikin kumgiyoyin.

Ngige ya kuma ce gwamnati ta matsu dalibai su koma makarantu, kuma shi ya sanya ma taronta na ranar Alhamis zai mayar da hanakali kan rahoton ci gaban da aka samu daga hukumomin da ke kokarin magance rikicin musamman ma NITDA, dangane da yadda aka yi da gwajin tabbatar da inganci ga tsarin biyan albashi na UTAS da ASUU ke son gwamnatin ta yi amfani da shi, madadin na IPPIS da SSANU da NASU suka gabatar.

Ministan ya ce yanzu haka dai yana jiran sakamakon rahoton kwamitin da ya hada da Ma’aiktar Ilimi ta Tarayya da Shugaban Ma’aikata, da albashi, da kudaden shiga, da ta kula da jami’o’i ta kasa, da kuma kungiyoyin da ke yajin aikin.