Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta bukaci Babban Akanta na Kasa, Ahmed Idris, ya yi wa ’yan Najeriya bayanin yadda ya mallaki wata kasuwa ta biliyoyin Naira da kadarori a Jihar Kano.
Shugaban ASUU reshen Jihar Bauchi, Farfesa Lawan Abubakar, ya kalubalance shi ya yi bayanin yadda ya sayi otel din Sokoto Hotel a Jihar Kano a kan miliyan N500, ya kuma umarci da a rushe shi washegarin ranar da ya siya da gina baban kasuwar sayar da kaya ta zamani.
- Mutum biyu sun mutu a rijiya a Kano
- COVID-19: An sake rufe makarantu a Amurka
- Masu garkuwa da ’yan uwa 5 a Abuja sun bukaci N30m
Kungiyar da ta ce yanzu haka ana kan ginin kasuwar a Kano ta kuma kalubalanci Babban Akantan ya yi wa ’yan Najeriya bayanin yadda ya samu kudin da ya gina kasuwar canji da kayan masarufi da ta lakume biliyoyin Naira a garin Gezawa, Jihar Kano.
ASUU ta ce: “Muna bukatar ’yan jarida su taimaka mana wurin binciko wadannan abubuwa guda biyu:
“Tambaya ta farko ita ce, waye ya sayi otel din Sokoto Hotel a Jihar Kano a kan miliyan N500 ya kuma biya kudi aka rushe ta washegari?
“Tambaya ta biyu kuma ita ce, wa yake ginin kasuwar zamani ta biliyoyin Nairori a Gezawa, Jihar Kano”.