✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

ASUU: Jami’an tsaro sun dakile yunkurin zanga-zangar dalibai a Kaduna

An girke jami’an tsaro a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja a matsayin wani mataki na hana dalibai gudanar da zanga-zanga kan yajin aikin da Kungiyar…

An girke jami’an tsaro a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja a matsayin wani mataki na hana dalibai gudanar da zanga-zanga kan yajin aikin da Kungiyar Malamai Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ke ci gaba da yi.

Shugabannin kungiyoyin dalibai daga manyan makarantu a Kaduna ne suka yi barazanar mamaye babbar hanyar a ranar Laraba don nuna fushinsun kan yajin aikin ASUU da ya ki ci, ya ki cinyewa.

A ranar Talatar da ta gabata gwamnatin Jihar Kaduna ta hannun Kwamishinan Kula da Harkoki da Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwan, ta gargadi daliban kan matakin tare hanyar da suka shirya dauka saboda dalilai na tsaro.

Wakilinmu da ya ziyarci babbar hanyar ta Kaduna zuwa Abuja, ya ga yadda aka girke jami’an tsaro a garin Gonin Gora don hana daliban cim ma kudirinsu.

Haka nan babu ko mutum daya da aka gani yana zanaga-zanga a yankin.

Daya daga cikin jagororin daliban, Kwamred Dominic Philip, ya ce sun janye kudirin yin zanga-zangar tun a ranar Talata bayan da Kwamishinan ’Yan Sandan jihar da sauran hukumomin tsaro suka sa baki cikin lamarin.

Kwamred Dominic ya ce ba shashanci ya sa suka janye shirin nasu ba, amma sun yi hakan ne gudun takura wa matafiya a hanyar.