Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, ya kira zaman sulhu tsakanin Gwamnatin Tarayya da kuma malamai da sauran ma’aikatan jami’a na Najeriya.
Gambari ya kira zaman ne bayan Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) ta tsawaita wa’adin yajin aikinta da wata uku bisa abin da ta kira gazawar gwamnati wajen biyan bukatun malaman jami’a da ta yi alkawari.
- NAJERIYA A YAU: Hatsarin Da Yajin Aikin ASUU Zai Jefa Najeriya
- 2023: PDP ta jingine karba-karba a kujerar shugaban kasa
“Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ne zai jagoranci zaman da zai gudana da misalin karfe 4.00 na yamma a dakin taro na Fadar Shugaban Kasa,” inji sanarwar taron.
Malaman sun yanke shawarar yin hakan ne bayan cikar wa’adin wata biyu da suka kwashe suna yayin aiki da sunan bai wa gwamnatin isasshen lokaci ta gama nazare tare da yanke shawara kan bukatunsu.
Ganin sun shiga sabon yajin aikin ne Gambari ya kira zaman da za a gudanar a Fadar Shugaban Kasa a ranar Alhamis da yamma, tare da ASUU.
Sauran mahalarta taron sun hada Kungiyar Ma’aikatan Jami’o’i (NASUU) da sauran kungiyoyi kwararru da na kwadago masu rajista a jami’o’in da suka shiga yajin aikin da ya tsayar da harkokin karatu cik a jami’o’in gwamnati.
Zuwa lokacin kammala wannan rahoto dai babu tabbaci daga kungiyoyin malamai da sauran ma’aikatan jami’ar game da halartar taron, wanda Ministan Kwadago, Chris Ngige, zai karbi bakunci.