Wasu dalibai a Najeriya sun fara kokawa kan yadda Gwamnatin Tarayya ke neman yin birus da mambobin Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU).
Daliban, wadanda suka zanta da Aminiya a ranar Lahadi sun bayyana lamarin a matsayin ‘abin damuwa’, duba da yadda ASUU ke barazanar sake tsunduma sabon yajin aikin.
Sai dai Ministan Kwadago da Ayyuka, Mista Chris Ngige, ya gayyaci shugabancin ASUU zuwa teburin sulhu domin kaucewa takaddamar da ke neman kunno kai.
Mai magana da yawun ma’aikatar, Charles Akpan, a wata hira da wakilinmu ta wayar tarho, ya bayyana cewa an shirya gudanar da taron ranar Litinin a hedikwatar ma’aikatar, da ke Abuja.
Za a fara taron da misalin karfe 2:00 na rana, kuma shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ne zai wakilci kungiyar, yayin da Minista Chris Ngige zai jagoranci tawagar gwamnati.
Aminiya ta rawaito cewar gwamnati da malaman jami’o’in sun dauki tsawon lokaci suna takaddama kan amincewa tsarin biyan albashi, da gwamnati ta fito da shi na EAA.
Hakan ya sanya ASUU tsunduma yajin aikin da ta shafe tsawon wata tara, kafin ta cimma yarjejeniya da gwamnati kan wasu bukatu da hakokkinsu.
Amma ASUU ta zargi Gwamnatin Tarayya da karya yarjejeniyar da ta kulla da malaman kafin su janye yajin-aikin da suka yi a ranar 24 ga Disamban 2020.
Ra’ayin dalibai
Wani dalibi a Jami’ar Bayero da ke Kano, Hassan Aminu, ya roki Gwamnatin Tarayya da ta sasanta batun tsarin albashin (IPPIS) tare da malaman a kan lokaci.
Ita ma, Saidat Akande, dalibar ajin digiri na biyu, a Jami’ar Ahmadu Bello, da ke Zariya, ta yi mamakin yadda gwamnati ta gaza kawo karshen takaddamar.
“Me gwamnati ke so a sake jefa jami’o’in Najeriya cikin yajin aiki da ba dole ba ne, gaskiya mun gaji,” a cewarta.
Wani dalibin Jami’ar Obafemi Awolowo, Ile-Ife, a Jihar Osun, Lukman Olalekan, a wata tattaunawa ta wayar tarho da Aminiya ya shawarci gwamnati da ta tabbatar jami’o’in kasar nan sun kasance masu cin gashin kansu.
Ya kara da cewa ya kamata a ba su hanyar da za su samar wa da kansu kudi kamar yadda ake yi a Turai da sauran sassan duniya.