✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

ASUU da gwamnati sun soke tattaunawar da za su yi kan yajin aiki

Daga karshe dai Gwamnatin Tarayya da ASUU sun sanar da soke tattaunawar da suka tsara yi.

Daga karshe dai Gwamnatin Tarayya ta sanar da soke tattaunawar da ta tsara yi ranar Litinin da kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) kan yajin aikin da suke yi.

Tattaunawar, wacce Ministan Kwadago Chris Ngige yake jagoranta don magance wasu batutuwa da suka ki ci suka ki cinyewa dai ya kamata ayi ta ne a makon da ya gabata amma aka sake dage ta saboda gaza cimma matsaya tsakanin bangarorin biyu.

Yajin aikin malaman jami’o’in dai wanda aka kwashe watanni tara ana yi ya samo asali kan saka su a tsarin biyan albashin bai-daya na IPPIS ya kassara harkokin ilimi a Najeriya.

Kakakin Ma’aikatar ta Kwadago, Charles Akpan shine ya tabbatar da dage tattaunawar, ko da yake bai yi karin bayani a kan musabbabin hakan ba.

Ya ce, “Barkan ku da war haka abokan aiki. Muna sanar da ku cewa tattaunawar mu da ASUU wacce aka tsara yi a yau an soke ta.”

Idan dai za a iya tunawa, Gwamnatin Tarayya yayin tattaunawar ta da kungiyar ranar 27 ga watan Nuwamban 2020 ta yi alkawarin biyan Naira biliyan 40 a matsayin kudaden alawus-alawus sai biliyan 30 a matsayin kudaden farfado da jami’o’i, adadin kudin da jimlar su ya kai biliyan 70 kenan.