✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

ASUU da Gwamnati sun daidaita

Shugaban ASUU Biodun Ogunyemi ya ce an samu biyan bukata a zamansu da gwamnati

Kungiyar Malaman Jami’a ta Najeriya (ASUU) da Gwanatin Tarayya sun daidaita kan muhimman batutuwan da suka sa malaman shiga yajin aiki na twason wata 10.

Bangarorin biyu sun cimma matsayar ce bayan sa’a takwas suna tattaunawar sulhun kan yajin aikin malaman jami’ar, inda suka daidaita kafin wayewar garin Laraba.

Bayan tattaunawar da Ministan Kwadago, Chris Ngige ya jagoranta a Abuja, ASUU ta bayyana gamsuwa da yadda gwamnati ta fuskanci al’amarin.

ASUU ta kara da cewa gwamnati ta kara musu sabon tayi, wanda kungiyar za ta tattauna a kansa sannan ta sake waiwayar gwamnati.

Tun watan Maris ne dai malaman jami’ar suka fara yajin aiki domin matsa wa Gwamnatin Tarayya ta cika alkawuran da ta musu tun  daga shekarar 2009.

Bukatun malaman sun hada da a biya su alawus din da suke bin gwamanti bashi, a biya albashinsu da aka rike, a samar wa jami’o’i isassun kudaden gudanarwa, yi watsi da maganar sanya su cikin tsarin biyan albashi na bai-daya (IPPIS) sannan a biya sa sauran alawu-alawus dinsu.

Gwamnati ta ba da kai

Tuni dai gwamnati ta amince ta biya malaman kudadensu alawus da yawansu ya kai Naira biliyan 40 da kuma Naira biliyan 30 na sauran alawus din.

Ta kuma amince ta yi gwajin ingancin tsarin biyan albashi na UTAS da malaman kungiyar ta gabatar mata.

Yanzu abin da ya rage shi ne Naira biliyan 30 na sauran hakkoki.

Sabuwar yarjejeniya ASSU da gwamnati

Bayan taron sirrin, Ngige da shugabannin ASUU sun ce an samu biyan bukata a zaman kuma kungiyar za ta tattauna da ’ya’yanta kafin su janye yajin aikin.

Shugaban ASUU, Biodun Ogunyemi ya tabbatar da cewa gwamanti ta yi wa kungiyar wani sabon tayi wanda kungiyar za ta tattauna a kai kafin ta tuntubi gwamanti daga baya cikin sa’a 24.

Janye yjin aikin ASUU

A sarfiyar Laraba ake sa ran ASUU ta fitar da sanarwa game da janye yajin aikin.

ASUU ta ce tana da tsarin da take bi kafin ta janye yajin aikin nata da ta shafe wata kusa 10 tana yi.