✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amfani da matsalolin Asusun TSA

Tsakanin amfani da matsalolin tsarin Asusun Ajiy na Bai-Daya (TSA) wanne ya fi yawa?

Asusun    Tattara    Kudin    Shiga   na   Bai-daya   da   gwamnatin     Shugaban     Kasa Muhammadu Buhari ta runguma ya kawo sauyi kan hanyoyin da ake bi wajen tara kudaden shigar gwamnati da yadda ake kashewa a matakin tarayya.

An bullo da tsarin ne domin dakile kafofin da ake bi wajen satar dukiyar kasa.

An kaddamar da Asusun Bai-Daya ko Treasury Single Account (TSA) a Turance, tun lokacin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan a shekarar 2012 a karamin mataki, inda bayanai suka nuna ya samar da raguwar sata na kimnain Naira biliyan 500.

Sai dai akwai masu korafin cewa tsarin yana jawo tafiyar hawainiya da tarnaki wajen tafiyar da ayyuka a hukumomi da cibiyoyin gwamnati.

Sukan kawo misali da cewa ko da Naira dubu 10 za a kashe a ma’aikata ko hukuma ta Gwamnatin Tarayya, sai an tura ofishin Akanta Janar da wasu ofisoshi sun amince kafin a saki kudin, lamarin   da suka ce yana kawo cikas ga bukatar gaggawa ta kashe kudi don gudanar da aiki.

Alherin TSA ya fi yawa – Masana

Aminiya ta tattauna da wasu masana tattalin arziki da masu bin diddigin yadda ake kashe kudaden gwamnati kan lamarin, inda suka ce duk da matsalolin da shugabanni da jami’an ma’aikatu a hukumomin gwamnati suke ganin tsarin yana dauke da su, suna ganin alherinsa ya fi yawa idan aka lura da yadda yake dakile almundahar da ake saba tafkawa a kasar nan.

Daya daga cikin wadanda Aminiya ta zanta da su kan batun wanda ya kai matakin Mataimakin Babban Akanta, Malam Idris Muhammad Augie, ya ce kafin fara amfani da tsarin, an kai lokacin da rukunan   asusun ajiyar Gwamnatin Tarayya kadai ya tasam ma guda miliyan daya.

“Zuwan Shugaban Kasa (Muhmmadu) Buhari ne ya rungumi cikakken amfani da tsarin,” in ji shi.

Tsaftace tafiyar da kudaden gwamnati

Malam Muhammad Augie ya ce amfani da tsarin ya tsaftace sha’anin   tafiyar da gwamnati inda take da masaniya kan adadin kudin da ke shigo mata da kuma fita a duk lokaci da ta bukata, kasancewar kudin na tattare ne a cikin asusu guda.

“A baya ma’aikata guda sai ta mallaki asusu sama da 100 a bankunan     kasuwanci, wasu asusun ma ba wanda ya san su sai babban jami’in da ke kula da asusun kawai.

“Ana shafe sama da shekara kudin gwamnati na jibge a wani asusu da ba nata ba, ana kwasar dukiya ana abin da aka ga dama ba tare da samun amincewar kasafi ba.

“A baya an yi lokaci da aka kididdige adadin kudin Gwamnatin    Tarayya da ke warwatse a asusun ajiya na bankunan kasuwanci da suka kai Naira tiriliyan biyu.

“Amma a haka sai ma’aikata ta karbo rancen kudi a bankunan, sannan idan aka tashi biya a dora masu kudin ruwa.” inji shi.

Dakile karayar arzikin gwamnati

Ya ce amfani da tsarin Asusun Bai-dayan ya taimaki gwamnati mai ci daga matsalar fadawa cikin mummunar karayar tattalin arziki, kasancewar ta zo ne a lokacin da darajar mai ta karye a kasuwar duniya, ga dokar kulle ta COVID-19 ga kuma koma-baya da aka fuskanta a bangaren hakar mai sakamakon fasa bututu a yankin Neja-Delta.

TSA ya hana sauya alkaluman kudade

Masanin bin diddigin kudi da tattara harajin ya ce tsarin biyan kudi ta Asusun TSA, ya kuma magance matsalar sauya alkaluma ta hanyar bambace abin da ke rubuce a rasidin wanda ya biya kudi da kuma  wanda  ake kawo wa gwamnati.

“Misali a rubuta Naira dubu 10 a kan rasidin da aka bai wa mai biyan kudi sannan wanda za a bai wa gwamnati sai a rubuta Naira 500.

“Ga tarin kudin da ake kashewa wajen buga takardun rasidan su kansu, inda wasu ke yin kudi ta wannan hanya.

Tsarin biyan albashi na IPPIS ya kawo tsafta

“Baya ga tsarin na TSA, akwai kuma tsarin biyan albashi mai suna Integrated Personnel and Payroll System (IPPIS) da gwamnati mai ci ta karfafa amfani da shi, wadanda duka sun taimaka,” in ji shi.

Da yake tsokaci a kan tsarin na IPPIS, Malam Muhammad Augie ya ce   amfani da shi ya taimaka wajen sanin adadin ma’aikata da matakan albashinsu.

Sannan idan lokacin biyan albashi ya yi, sai kowane ya ga shigowar kudi ta asusun ajiyar da ya ba da.

Ya ce hakan ya saba da tsarin baya inda kowace ma’aikata ke biyan albashinta da kanta.

“Misali adadin ma’aikata ba su wuce mutuum 50 ba, amma sai a rika karbar albashin kamar mutum 80.

“Wasu ma’aikatan bogi ne wasu kuwa ma’aikatan gaskiya ne, amma sun yi ritaya ko sun rasu, amma sai ka ga duk wata ana fitar da albashi da sunansu,” in ji shi.

‘Tsaikon da TSA ke haifarwa ba sabon abu ba ne’

Da yake tsokaci a kan tsaiko da tsarin yake haifarwa kafin a kashe kudi komai kankantarsa a ma’aikata ko hukuma, masanin tattara harajin da   kuma bin diddigin kudi, ya ce, “Ai dama tsarin gudanar da gwamnati ya gaji hakan, komai sai an rubuta a sa hannu a nan, a sa a can.

“Da za a yi kidayar ma’aikatan haraji da na biyan albashi da gwamnati ta samu sauki wajen daukar nauyinsu kafin wannan tsarin tattara harajin.

“A kuma kididdige munin  almundahanar da ake tafkawa a wuraren,  to  lallai sai masu wannan sukar sun gode wa wadanda suka kirkiro sabon tsarin, sannan su manta da batun tsaikon da suke ganin tsarin na haifarwa,” in ji shi.

Jihohi ba rungumi tsarin TSA ba

Sai dai ya ce abin takaici har yanzu jihohi da dama ba su   rungumi   tsarin   ba, inda ya bayyana Gwamnatin Jihar Kaduna a matsayin daya daga cikin jihohi da yake da tabbacin ta rungumi tsarin, lamarin da ya ce ya taimaka wa gwamnatin jihar wajen kyautata kudin shigarta.

Ya bukaci gwamnati ta inganta tsarin ta hanyar kyautata layukan sadarwa da ake amfani da su, wadanda ya ce akan samu tsaiko ta wannan dalili a mafi yawan lokuta.

TSA ba sabon abu ba ne

Aminiya ta kuma tuntubi wani tsohon Darakta a Bangren Kudi na ma’aikatun Gwamnatin Tarayya, mai suna Malam Ibrahim Ali, wanda mamba ne a Kungiyar Akantoci ta Kasa (ANAN), inda ya ce, kodayake tsarin sabo ne a matakin gwamnatin kasar nan, amma dadadden abu ne a harkar tsarin bin diddigin kudi da wasu kasashen duniya suka jima suna amfani da shi.

“Babbar manufar tsarin ita ce a tafiyar da kudin gwamnati a dunkule ta yadda za ta ba da damar tsimi da tanadi da kuma yi wa sha’anin tafiyar da kudin linzami domin toshe duk wata kafar barna ko salwantar kudin gwamnati.

“Ma’ana duk kudin da ke shigowa ko fita za a iya bin diddiginsu a cikin sauki,” in ji shi.

Ya kara da cewa: “A lokaci guda jagoran gwamnati zai iya sanin adadin kudin da ke cikin lalitar gwamnati da kuma gane wa kansa yadda suke shiga da fita a cikin sauki.”

Gagarumin cigaba

Malam Ibrahim Ali ya ce an samu gagarumin ci gaba a fuskar samar da kudin gwamnati tun fara amfani da tsarin sabanin baya inda ba a sanin   wasu   asusun ajiyar ma dungurugum, sakamakon yadda ake hada baki a tsakanin jami’an gwamnati da na bankuna ana    tafkamalmundahana.

Ya ce haka kuma su kansu masu binciken kudi wato oditoci ko   hukumomin yaki da almundahana za su samu sauki wajen gudanar da aikinsu kasancewar asusun sananne ne kuma a dunkule waje guda, sannan duk wani da aka samu a bayansa ya bayyana cewa na almundahana ne.

Ya ce akwai ma’aikatun gwamnati da dama da ba na samar da kudi ba ne, sai dai bukatarsa kamar Ma’aikatar Tsaro, kamar yadda ake da   hukumomi da babban aikinsu shi ne samar da kudin kamar Hukunmar Tattara Haraji ta Kasa da Hukumar Kwastam.

Ya ce, kowanensu zai gabatar da bukatarsa ce don amincewar ma’aikatarsa, wani matakin kuma sai ya kai gaban taron Majalisar Zartarwa na mako-mako.

Ya ce sai dai akwai bukatar gwamnati ta waiwayi wasu bangarori irin cibiyoyin  lafiya da hukumomi  irin na samar da ruwan sha don tsara   masu  hanyoyin  kar-ta-kwana  a duk lokacin  da suka bukaci daukin gaggawa.