A fafutukar da ake yi wajen samar da sana’ar neman abin gudanar da rayuwa ga mutanen da suka jikkata sanadiyyar kunar bakin wake a Arewa maso Gabas, inda Asusun tallafa wa wadanda suka jikkata na bSF ya rarraba tumaki da kudi ga wasu manoma da aka zabo daga karamar Hukumar Geidam da ke Jihar Yobe.
Kayan tallafin da suka hada da dabbobi 800 an raba su ne ga iyalai 200 da aka zabo daga al’ummomi Hausari da Ashekari da Koloro da Geidam. A wajen kaddamar da raba kayan tallafin a garin Geidam, inda babban daraktan Asusun bSF, Farfesa Sunday Ochoche ya bayyana al’amarin a matsayin ci gaba da shirin bayar da tallafin noma ga manoman Arewa maso Gabas na shekarar 2017, inda ake ayyana taimakon iyalan da suka jikkata. Ya bayyana cewa an bullo da shirin bayar da agajin ne don tallafa wa rayuwar mutanen da suka jikkata suka samu abin gudanar da rayuwa a al’ummominsu, tare da kokarin wadata yankin da abinci na tsawon lokaci.
An fara kaddamar da shirin bayar da tallafin noman ne a kananan hukumomin Gulani da Gujba, inda aka tallafa wa iyalai dubu biyu (2000), wadanda suka samu kayan aikin gona. Farfesa Ochoche ya ce Asusun bSF ya gamsu da kyakkyawan sakamakon da shirin ya haifar, sannan ya samu kwarin gwiwar fadada shirin ta yadda za a kawo dauki a harkar noman rani da tattaro karin jama’ar da za su ci gajiyar shirin, ta hanyar raba musu kayan aikin gona da kudi. A cewar Farfesa Ochoche, kowane iyali sun karbi awaki hudu, awaki uku da bunsuru guda, tare da Naira dubu 20 a matsayin tallafin fara sana’a don a saukake harkar kiwon dabbobi.
Ya nuna farin cikinsa kan yadda Gwmanatin Jihar Yobe ta hada gwiwa da su, sannan ya yi alkawarin cewa Asusun bSF zai jajirce wajen hadin gwiwar don ci gaba da gina yankin.
Shi kuwa shugaban Kwamitin PCNI Laftanar-Janar TY danjuma, wanda ya samu wakilcin Alkasim AbdulKadir ya karfafa gwiwar mutane kan lallai su zauna lafiya da juna, sannan ya ba su tabbacin cewa za a ci gaba da aikin sake gina yankin, har sai an samar da kayan more jin dadin rayuwa da farfado da tattalin arzikin yankin, ta yadda za a cimma samar da dimbin ayyuka. Gwamnan Jihar Yobe, Ibrahim Gaidam, wanda ya samu wakilcin Kwamishinan Ilimi Mohammed Lamin ya yi godiya ga Asusun bSF bisa daukin da suka kawo na tallafin dabbobi, inda ya yi nuni da cewa sun kawo a kan kari, kuma tallafin zai tallafi rayuwar al’ummar da ake nufi, ta yadda za su samu abin gudanar da rayuwa na yau da kullum.