✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ashe Turawa mutane ne? (6)

kila yanzu wasu na iya tambayar me ya kawo ne Landan? Amsar ba wuya gare ta ba. Haduwa ce a birnin Kano ta tayar da…

kila yanzu wasu na iya tambayar me ya kawo ne Landan? Amsar ba wuya gare ta ba. Haduwa ce a birnin Kano ta tayar da zuwan nawa Ingila. Taro ne na masana harkar adabin Hausa daga jami’i’o’i daban-daban a birnin na Kano. Nan ne na gabatar da wata kasida, wadda ta dan burge masu saurare. A cikin masanan akwai wani Farfesa daga Jami’ar Landan da ya zo wajen taron, ya ji dadin abin da na gabatar, mun tattauna da shi, ya nuna mani cewa akwai wasu ayyuka makamantan wannan da na tattauna a Ingila, da zan karanta su, zan kara samun haske kan wannan fage da nake bincike a kai. Nan take muka kulla zumunta, ya kuma ba ni adireshin da ya ce zan aika da batuna, za su iya daukar nauyina zuwa Ingila, sai dai ya nuna mani cewa gasa ce ake yi duk shekara, don haka ba garanti, mai rabo ke samu.
Ni dai na amshi adireshin amma ban ma tuna da batun ba sai can bayan an dade da watanni a cikin watan Afrilu na 2007, lokacin saura wata daya a rufe amsar batutuwan gasar. Kamar dai in fasa ganin kila na yi latti, haka nan na aika masu da batuna da kuma ko ni wane ne da irin yadda nake so na amfana da wannan dama. Kafin a rufe wannan karvar batutuwan gasar ranar 1 ga watan Mayu 2007, na samu labarin cewa sun ga sakona, sai na koma na ci gaba da rayuwata. Duk abubuwan da ake yi ta Imel ne, wato Intanet, saboda haka ba wata matsala ta rashin sanin abin da ake ciki, sai dai in ba komfuta, ba kuma Intanet.
A ranar 6 ga watan Yuni 2007 na samu sako daga Sakatariyar Cibiyar da ke gudanar da gasar cewa “Bayan an bi duk takardun da aka aiko domin shiga wannan gasa daga Najerya, an kuma tattauna duk batutuwan da kowa ya aiko, an kuma dubi ayyukan da kowa ya yi a rayuwa, kwamitin tacewa da daukar masu zuwa binciken wata uku na Leventis da Jami’ar Landan, karkashin jagorancin Farfesa Murry Last, na farin cikin bayyana maka cewa ka samu gurbi daya daga cikin biyu da aka ware wannan shekarar, muna tsimayarka a watan Satumba na 2007. Kuma za mu aiko maka da tikiti da sauran bayanai nan gaba kadan. Kuma za ka zauna tare da mu daga ranar 15 ga Satumba zuwa 15 ga Disamban 2007.”
Bari na yi abin gwari-gwari domin a gane dukkan irin wannan kai-kawo da nake ta yi. Shi wannan zama da ake bayani, na bincike ne da karatu da ziyarce-ziyarce (ko kuma na karatu da yawon bude-ido) da gabatar da kasidu da halartar tarurrukan kara wa juna sani da leka wuraren sayar da littattafai da ajiye su da dai makamantan wuraren karuwar ilimi. Kana iya cewa wannan balaguro wata ’yan makaranta ce mai tarin muhimmanci, kuma dama ce da duk wani malami zai so ya samu domin zuba wa tukunyar iliminsa ruwa masu albarka.
Sauran batutuwa da ma can na yi muku bayani, saboda haka a wannan safiya  da na wayi gari a Landan ba abin da na yi sai faman neman gano inda mazaunin jami’ar yake. Tun a masauki na tambayi budurwar da ke gaban teburin amsar baki ko yaya zan gano inda School of Oriental and African Studies, University of London, take, nan take ta yi man kwatance, ta ce da na fita, in yi dama zuwa bakin titi, in dubi yamma sai in mike in yi ta yi, ta ce har cikin jami’ar ba zan vace hanya ba. Ina fita kuwa na doshi yamma kamar yadda ta ce da ni, ina yin kamar tafiyar minti biyar sai ga ni a Russell Skuare, unguwar da  jami’ar take. Na dade da sanin unguwar ko dai ta wasiku ko kuma ta Intanet shekaru da suka wuce. A daidai wannan wuri ne dubban mutane suka sha da kyar a lokacin da aka sanya bama-bamai a tasoshin jiragen kasa na karkashin kasa a shekarar 2005, inda  bam uku suka fashe da misalin karfe takwas na safe, tsakanin tashar Liverpool da Edgware da kuma tsakanin King Cross zuwa Russell Skuare. Daga baya kuma wani bam din ya fashe a bisa wata bas mai hawa biyu a tashar Tavistock, kusa da King Cross ita ma. ’Yan kunar bakin wake ne su hudu aka ce suka saki wadannan bama-bamai a ranar 7 ga watan Yulin 2005, inda mutum 52 suka mutu, sama da 770 suka jikkata.
Saboda haka koda na iso wurin, idanuna na kai-da-kawo ko zan sake ganin an yiwo waje da gudu, wai ko wani bam ya sake tashi saboda tun a gida ake yi man bayanin fashewar bama-bamai a unguwar. Haka kuma duk wata doguwar bas da na gani mai hawa biyu sai na yi nesa da ita, ina tunanin ko akwai bam a ciki. Kafin dai na kai cikin jami’ar, wadda ba ta nesa da tashar Russell sai da na ga bas-bas irin waccan da bam ya fashe sun kai goma, kowa na ta kai-da-kawo cikinsu, daga nan ne na fahimci cewa su ma ’yan kasar sun fara mantawa da abin da ya faru, balle ni da zuwana ke nan! Wai abin da Hausawa ke cewa fin mai kora shafawa!
Ginin Jami’ar Landan da na makarantar SOAS, kamar yadda aka fi kiranta, ke ciki ba wani abin tokabo ba ne, amma kuma ya tsaru, idan mutum ya tava shiga Senate Building na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, zai ga cewa tamkar haka wurin yake, sai dai kowa da komai na cikin ginin ne, cikin tsari da tsaro da kuma inganci.
Na yi kamar minti biyar ina kallon ginin kafin na shiga, domin kuwa gini ne na tarihi. An samar da shi tun a shekarar 1836, shekara daya da rasuwar Sarkin Musulmi Muhammadu Bello na Daular Usmaniyya a Najerya. Sai dai ita wannan makaranta ta SOAS daga baya ta samu, an kafa ta ne a 1916, shekara biyu da samuwar kasarmu Najeriya. An kudurta ne ta kasance cibiyar nazarin al’amurran da suka shafi Nahiyar Asiya da Afirka da kuma Gabas ta Tsakiya, bisa wannan fage ne ta yi suna duk duniya!