✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ashe Turawa mutane ne? (1)

Wannan labari da zan kawo a yau ya faru ne kusan shekara 7 da suka wuce, kuma duk da tsawon lokacin da aka dauka sai…

Wannan labari da zan kawo a yau ya faru ne kusan shekara 7 da suka wuce, kuma duk da tsawon lokacin da aka dauka sai na fahimci cewa lallai rayuwa kamar tsaye take, ba ta motsawa, domin abubuwan da suka sarke rayuwar tawa cikin shekarun ba su canza ba, ba sa kuma da alamar canzawa. Wannan na daga cikin dalilan da ya sa na ce bari na sake waiwayar tafiyar nan na ga ko za mu sake tsintar dami a kala.
Labaran da kullum ke zuwa mana daga kasashen Turawa mu da ke  zaune a kasashe masu tasowa shi ne a kasashen Turai komai na tafiya daidai ne, ba ka gani ko jin irin tabargazar da muke tafkawa a kasashe masu tasowa. Saboda tsari da yadda al’amurra ke gudana a kasashen Turai da Amurka ya sa wasu suke ganin cewa ai kila Turawa ba mutane ba ne kamar mu bakar fata ko kuma wadanda suke zaune a kassashe masu tasowa.
Ba sai na fada ba dai, kowa ya san irin yadda muke gudanar da lamuranmu a kasashenmu, rashin ajiyewa da tabbatar da lokaci ga mutumin Afirka ba wani abin damuwa ba ne. Rashin da’a da keta lamuran doka ba wani abin ka-ce-na-ce ba ne gare mu. Cin hanci da rashawa da almundahana da babakere da dukiyar jama’a a tsakanin shugabanni da mabiya ya riga ya yi mana katutu, haka kuma ya riga ya zame mana kwalliya. Rashin zaman lafiya da tashe-tashen hankula ba wani abin da zai daga mana hankali ba ne, balle har ya dame mu. Idan ba mu yi irin wadannan ba, kila sai mun kwana ba mu yi barci ba, ko kuma mu samu rashin lafiya. Kai idan mutum ya ce zai tsaya ya rattaba abubuwan da muke fama da su na lalaci da batanci da sakarci da wautanci da makamantansu sai ya cika littafi guda, domin kuwa da alama wadannan abubuwa sun zama ruwan dare a rayuwarmu.
To amma wannan ba yana nufin cewa mun fi kowa lalacewa ba ne ko kuma ba wani abin kwarai dangane da rayuwa irin tamu, ko alama! Rayuwa kowace iri ce da irin nata matsalolin da kuma ayyukan alheri da ke tattare da ita.
Wannan tunani ya zo mani ne a lokacin da na samu kainana zuwa kasar Turai a karo na farko. Na bar Najeriya ne da tunanin cewa zan je kasar Ingila, kasar da ta yi wa Najeriya mulkin mallaka, kasar da ta kwashe mana dukiya ta gina kanta da sauran kasashen Turai. kasar da ita ce ta shayar da mu mama. kasar da ake cewa  ta ci gaba fiye da kima. Tun ina gida Najeriya nake da tunanin cewa ba yadda za a yi a ce wani dan Adam ya fi wani saboda launin jiki ko fata ko saboda iya mulki ko siyasa ko kuma saboda addinin da mutum ke yi ko bi. Ban taba yarda cewa dan Afirka bai iya hus ko kuma ’yan kasashe masu tasowa ba su iya tabuka komai saboda yadda Allah Ya yiwo su ko kuma inda suka samu kansu ba. Kullum tunanina shi ne idan ka ba mutum dama da hadin kai da kayan da zai yi aiki da su, to shi ma zai iya ciyar da kansa gaba kamar kowa, domin ba al’ummar da aka halitta a matsayin malalaciya ko sangartacciya sai wadda ta gina kanta a bisa wannan tsari bayan halitta.
To, amma kuma dole ne ka yaba wa al’ummar da ta dage ta ci gaba da gudanar da rayuwarta bisa tsari da inganci da kyautatuwa a lokacin da wasu al’ummun ke ta faman ja baya da lalacewa. Me ya sa na ce haka?
Ban da wata hujja face tunanin da nake da shi na cewa ba wata al’umma da ta fi wata sai wadda ta mayar da kanta baya ko butal! Ban taba ganin abin da Bature ya yi da zan ce ya burge ni ba, saboda na kasance dan Najeriya, sai dai in ce dama ce kurum ya samu, idan na samu irinta ni ma sai na wuce shi fintinkau. To amma akwai abubuwa da har yanzu ba yadda za mu iya yi da su, domin kuwa suna tare da mu tamkar jini da tsoka ne, duk yadda ka yi da jaki sai ya ci kara.
Saboda haka koda na isa filin jirgin saman Abuja domin tashi zuwa Ingila, wannan tunani na tare da ni, na kuma sha badakala da tunanina game da ko a Najeriya nake ko kuma Ingila? Wane irin tsari zan yi aiki da shi, zan bi na gida Najeriya ko na Ingila da za ni? Wane irin tsarin lokaci zan yi aiki da shi na Ingila ko na Najeriya? Wane irin yanayin zamantakewa zan yi amfani da shi, namu na gida ko na Ingila da zan isa? Duk wadannan suna cikin tunane-tunanen da na isa da su filin jirgin  sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja domin zuwa Ingila. Sai dai kamar yadda ake fada, duk yadda ka yi da jaki sai ya ci kara. Duk da cewa na iso filin jirgin saman awa uku kafin jirgin British Airways ya iso Abuja, sai da na yi halin namu na ’yan Najeriya; an yi kira da a isa ga jirgin da misalin karfe 7:30, ni dai ina zaune, tunanina shi ne ai shi ma jirgin kamar na Najeriya ne ba zai tashi kan lokaci ba, duk da cewa an ce takwas da rabi zai tashi a jikin tikitin da aka aiko mani daga Ingila ta Intanet. Muna ta hirarmu, sai da na ji ana cewa masu zuwa Ingila su hanzarta domin jirgin British Airways na shirin tashi sa’annan na gane kurena, domin kuwa da ya tafi ya bar ni a tutar babu. Nan ne na fara amsar darasi na farko, cewa ba Najeriya nake ba, duk da cewa a Abujan Najeriya nake, amma da yake harka ce ta Turawan Ingila ba bakar fatar Najeriya ba, koda na ruga domin shiga jirgin sai na iske cewa kowa da ke wurin yana neman Ibrahim Malumfashi ne da ganin na azzamo a guje Turawan da ke wurin suka yiwo caa gare ni, tambayar da suke yi ta kare, domin kuwa ni kadai ake jira ba kuma wani Ibrahim Malumfashi, sai ni; haka na ruga daga wannan tebur zuwa waccan, sa hannu a nan, sa a can, amshi waccan takarda a hannun wancan , mika wa wancan; kafin na ankara sai ga ni cikin jirgin, ban ko shirya ba.
Sai da na zauna bisa kujerata ne na fahimci cewa na yi aiki da tunanina na dan Najeriya ne, ba wanda ke niyyar zuwa Ingila ba, da kuwa an tafi an bar ni, domin kuwa na hangi wata Baturiya dauke da jakar wani, tana cewa wannan mun yi ‘uploading’ dinsa. Na yi ajiyar zuciya na ce, ni ma da haka za a sauko da kayana, idan da na kara minti daya. Domin kuwa cikin ’yan mintoci, jirgi ya shirya, ya natsa, ya janye bakinsa daga jikin kofa, ya yi ribas, ya nemi hanyar fita; ina duba agogona kuwa na ga takwas da minti ashirin da biyar, ko kafin na ankara muna bisa iska, dokin Bature ya yi sama da mu zuwa Ingila cikin lokacin da aka ce, bisa lokacin da aka tsara, kuma ba tare da jiran wani ko wata ko wasu ba!
Wannan shi ne abu na farko da na fara yin la’akari da shi game da zuwana Ingila da kuma nazarin rayuwar mutanen da na iske a can. Wato dole ne in canza daga bakar fata zuwa Bature, ko ina so ko ba na so! Amma shin zan iya?