Ina mamakin irin mazajen da ke cika baki suna cewa su ba za su yi wa mace hidima ba, su mace ba ta isa ta juya su ba, saboda sun mance cewa tun asali shi namiji tare da mace aka halicce shi, kuma rayuwarsa ba ta cika sai da ’ya mace.
A ganina irin wadannan mazaje suna yaudarar kansu ne kawai, har gara su mika kai bori ya hau a maimakon su rika yi wa mata girman kai da nuna musu kiyayya da bambanci da kuma kyama.
Kodayake wadansu mazajen cika baki kawai suke yi a bainar jama’a, amma da sun koma gida sun kadaita da matansu sai ka sha mamakin irin yadda matansu ke juya su kamar waina a tandar suya.
Babu jayayya Allah Ya yi wa mata baiwa, kuma ya ba su akalar juya da namiji amma kuma shi da namiji an ba shi ikon jagorancin ’ya mace a hannunsa, sannan Ya bambanta shi da mace ta hanyar halitta da karfi da kuma juriya fiye, to amma duk da haka shi aka dorawa kula da ita da daukar dawainiyarta da kuma yi mata hidima domin ta ji dadi.
da namiji aka dorawa kula da gida ta hanyar nemo abinci da sutura da kula da lafiya, mace ita ce mai kula da tsaftar gida da wani bangare na tarbiyyar yara da reno da daukar ciki da kuma shayarwa. Ka ga tun a nan namiji ya zama bawan mace. Domin babu wanda ya dora mata dole sai ta nemo abinci. Asali ma komai kudinta mijinta ne zai nemo mata abin da za ta ci. Kuma ko da aure aka zo a daurawa za a ce wa mijin ciyarwa da tufatarwa da kula da lafiya hakkin miji ne. Ka ga a nan mace ta zama ’yar lele kuma ta zama ’yar hutu.
Shi ya sa idan na ga saurayi ko mai aure yana daga wa mata kai sai na rika tausayinsa, domin idan da ya fahimci yadda rayuwa ta ke ba zai daga mata hanci ba, sai dai ma idan ya gan su ya rika karrama su da girmama su.
Shi ya sa idan na ga namiji ya mutunta matarsa har a kan haka ana cewa ta mallake shi, ba na zarginsa kuma ba na ganin laifinsa. Wani lokaci biyayyar da matar take yi masa ne ya sa saboda jin dadin zama da ita sai ya rika tarairayar ta tare da girmama ta.
Ko da yaki za a je maza su ne a gaba. Su ne masu shiga a yi gumurzu, kuma su ne ke shiga filin daga su gwabza, su mata sai dai su lura da masu rauni da kuma kawo agajin jinkai da abinci da kuma abin sha. Kuma ma idan aka samo ganimar galibi su ake kowa wa su amfana da ita, domin kowane mutum da ya je yaki matarsa zai kawowa rabon da ya samu.
Kada mutane su yi mini mummunar fahimta. Ba ina nufin shi da namiji ba shi da wata kima ko wani matsayi ba, a’a ina nufin shi ma namiji Allah Ya karrama shi kuma ya ba shi kima, amma duk da haka nauyin kula da mace yana kansa.
Shi ya sa nake kira ga maza ’yan uwana su gane cewa bai kamata mu rika wulakanta mata ba, saboda iyayenmu ne, matanmu ne kuma ’yan uwanmu ne. Kamata ya yi mu hakura mu yarda cewa mu masu yi musu hidima ne tare da kula da su da daukar dawarniyarsu.
Ana bukatar mu mayar da su tamkar gwal ko zinare, mu kare musu hakkinsu, mu tsare musu mutuncinsu, mu yi musu duk abin da suke bukata, mu tausasa musu, mu yi musu ladabi da biyayya kamar yadda ya kamata.
Su kuma mata kamata ya yi su gane cewa maza ’yan uwansu ne abokan zamansu, su sani rayuwarsu ba za ta yi dadi ba sai da maza, kada su dauke su abokan gaba da gasa. Su rika yi musu biyayya da girmama su da yi musu ladabi. Ta haka ne za a samu zaman lafiya da dorewar soyayya da wanzuwar zaman lafiya da samun al’umma ta gari. To idan haka ne ashe maza bayin mata ne?
Za a iya samun Abubakar Haruna, ta lambar waya kamar haka: 08027406827 ko kuma [email protected] ko [email protected]
Ashe maza bayin mata ne?
Ina mamakin irin mazajen da ke cika baki suna cewa su ba za su yi wa mace hidima ba, su mace ba ta isa ta…