✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ashe ba ni ba ne

Wani Buzu ne falke, ya rika bugun gaba yana cewa shi babu wanda ya isa ya yi masa sata. Ashe wani babban barawo ya ji…

Wani Buzu ne falke, ya rika bugun gaba yana cewa shi babu wanda ya isa ya yi masa sata. Ashe wani babban barawo ya ji haka, don haka sai ya sha alwashin sai ya yi masa sata. Wata rana an ci kasuwa, Buzu ya sayar da kayansa duka, sai barawon nan ya sace masa kudi, ya bar shi da rakumi kadai, sannan kuma ya yi masa aski kwal-kwabo, a lokacin da yake barci. Da safe, Buzu ya tashi ya ga cewa an yi masa sata sai ya yi ta mamaki, yana cewa: “Ni din ne za a yi wa sata? Can sai ya shafa kansa ya ji ba gashi, sai ya ce: “Haba, ashe ma ba ni ba ne!”

Daga Ameer Umar Gummi, 08060322272