Tuwon Sallah kamar yadda sunan ya nuna tuwo ne da ake yi a ranar Sallah Karama ko Babba don nuna murna da farin ciki ga zagayowar ranar.
Ko da yake, idan an ce Tuwon Sallah ba wai ana nufin tuwo kadai ba, ana nufin abincin Sallah, sai dai ana kiran abincin da Tuwo ne kasancewar a wancan lokaci al’umar Hausawa shi suka fi girkawa.
- Kwalara ta kashe mutum 30, wasu 2,000 na asibiti
- An sauke shugaban makaranta saboda ya ba dalibai hutun Sallah
Sai dai daga baya ana girka duk wani nau’in abinci a matsayin abincin Sallah, wanda ya hada da Waina ko Funkaso ko Shinkafa da miya ko dafa-duka ko Alkubus da sauran nau’o’n abincin.
A baya, an fi yin Tuwon Shinkafa kasancewar a wancan lokacin Shinkafa sai gidan masu hali ake ganinta, don haka sai Hausawa suka dauke ta a matsayin sakakken abinci wanda ba ko yaushe ake ci ba kamar yadda wata dattijuwa Malama Rabi Muhammadu ta shaida wa Aminiya.
Ta ce, “Kin san a da ba ko yaushe ake cin shinkafa ba, yawanci an fi yin Tuwon Dawa ko na Alkama ko Masara da sauransu.
“To hakan ya sa idan za a yi abincin Sallah to za ki samu Tuwon Shinkafa ne wanda za ayi masa miyar Taushe wacce aka sa mata nama.
“Wasu ma za ki ga idan da wadata har kaji suke yankawa a zuba a cikin girkin,” inji ta.
‘Ana raba wa makwabta da ’yan uwa’
A cewar Malama Rabi, yawanci akan raba abincin Sallar ga ’yan uwa da abokan arziki duk don murnar Sallah.
“Dama ana yin abincin mai yawa saboda raba shi ga ’yan uwa da abokan arziki. Idan aka gama Tuwon za a aika yara su kai abincin gidajen ’yan uwa da abokan arziki na kusa da na nesa.
“To hakan ya sa sai ku tara abinci da yawa a gida wanda ka samu daga gidaje daban-daban. Saboda yawan abinci sai ku yini kuna ci har dare.
“Ma’ana wannan abincin Sallar da aka girka da safe shi za a ci a matsayin abincin rana da na dare.”
‘Yana cikin abin da ke kara wa Sallah armashi’
Wata matar aure mai suna Malama Aisha Inusa ta bayyana cewa shirye-shiryen Tuwon Sallah da ake yi ranar jajiberi na daga cikin abin da yake sanyawa mutum ya san cewa da gaske Sallar za a yi.
“Saboda wanann hidimar girkin da ake fara yi tun yamma, ina iya tunawa ranar jajiberi babanmu zai aiko da cefane daga kasuwa, dukkaninmu ’yan gidan da iyayenmu sai kowa ya kama aikin da zai yi, yayin da wasu ke gyaran kayan miya, wasu kuma su mayar da hankali wajen gyaran nama tare da dora shi a wuta, wasu kuma gyaran Kabewa da Alayyahu ko dakan Gyada da sauransu.
“Haka kuma, kasancewar yawancin shinkafar da ake yi Tuwon da ita ta gida ce wacce ke bukatar gyara sai wasu daga cikin ’yan gidan su zauna su gyara shinkafar da sauransu.
“Haka za a yi ta aiki har dare. To wannan aikin da ake yi yana daga cikin abin da yake tabbatarwa mutum cewa gobe Sallah da sauransu.
“Kuma a wancan lokaci kusan kowane gida kika shiga abin da za ki tarar ana yi ke nan.”
Malama Aisha ta yi wa Aminiya karin haske game da yadda tuwon Sallah ke kara wa sallah armashi.
“Kasancewar a ranar Sallah sai ki sami abincin Sallah daga gidaje daban-daban kimanin goma sha, wannan ya kan sa mutum ya rika nishadi tare da samun karfin gwiwar son cin abinci saboda mutum sai ya zaba ya darje kafin ya ci.
“Ina iya tunawa a wancan lokaci har mun san abincin gidajen da suka fi dadi don haka za ki tarar rububin wannan abincin ma muke yi.”
Yanzu akan hada har da kayan makulashe
Bincike ya nuna cewa a yanzu haka, baya ga abincin Sallah da ake yi ko masu hali sukan hada da kayan makulashe da suka hada da cincin da kek da sauransu.
Haka kuma, ana girka naman kaza a soya don a kara wa bikin na Sallar armashi.
Hajiya Hadiza Bello dattijuwa ce mai kimanin shekara 80, ta bayyana wa Aminiya cewa duk da cewa ba za ta iya fadin lokacin da aka fara Tuwon Sallah ba, amma dai ta san tun tana yarinya ake yi haka har zuwa lokacin da ta yi aure ta fara tukawa a gidanta.
Dalilai biyu ke hana mutane yin Tuwon yanzu
Sai dai ta bayyana cewa a yanzu lamarin ya canza salo kasancewar yawancin magidantan ba su yin abincin Sallah saboda wasu dalilai.
“Ba kamar ada ba wanda kusan kowane gida idan ka shiga ana yin wannan Tuwon Sallah, daidai karfin maigidan.
“Duk da cewa ana kawo wa mutum daga gidajen makwabta amma hakan bai sanya shi ya ki girkawa ba.
“Kowa kwadayin samun ladan yake. Amma a yanzu idan kika kula abubuwa biyu ne ke sanyawa aka rage yin Tuwon sallah.
“A wasu wuraren matsin tattalin arziki da ake fuskanta ya janyo magidanta ba su iya yin cefanen Tuwon Sallar. A bangare daya kuma wasu matan kyuya ce ke hana su su yi.
“Sai ki ga idan ya kasance ma za a yi Tuwon to za a yi shi ne daidai bukatar mutanen gidan sai kuma wanda ya shigo gidan don ziyara. Amma ba a raba shi ga makwabta ballantana dangi na nesa.
“Mu a wancan lokacin Wallahi so muke yi ma a kawo aikin tuwon sallah din domin mu yi mu ba iyalinmu da sauran ”.
‘Bana yi saboda ana kawo min’
Wata matar aure mai suna Hauwa Sulaiman ta bayyana cewa ita gaskiya ba ta iya yin abincin Sallah saboda ana kawo mata daga gidan iyayenta da na mijinta.
“Gaskiya ni ina ganin yin wannan abincin kamar wahalar da kai ne. kin san Allah ko na iya gidan ma ba na girkawa saboda ana kawo min daga gidanmu.
“Haka kuma ana kawowa daga gidan su maigidana . To mu kanmu ya yi mana yawa sai na bayar. Kuma ni gaskiya ba zan iya yin abincin ina wani aikin rabonsa a makwabta ba. Abin da nake yi shi ne in yi cincin da kek da lemo. Idan na yi baki na zuba musu,” inji ta.
‘Al’ada ce mai kyau’
Wani malami a Sashen Koyar da Harsunan Najeriya a Kwalejin Ilimi ta Tarrayya da ke Kano, Dokta Bashir Ibrahim ya bayyana cewa al’adar yin Tuwon Sallah al’ada ce mai kyau wacce Bahaushe ya fara yin ta shekaru masu yawa wanda kuma za a dade ba tare da ta ruguje ba duba da cewa tana da dangantaka da Addinin Musulunci.
“Idan kika dauki wannan al’adar za ki ga tana da alaka da addinin Musulunci wanda kuma shi ne addinin da mafi yawan Hausawa suke bi a kasar Hausa.
“Misali, ki dauki batun kyauta a addini da kuma yalwatawa iyali abubuwa ne da addinin Musulunci ya yi umarni da su don haka za a dade ba a shafe ta a doron kasa ba.
“Duk kuma da cewa a yanzu wasu na kin yin abincin Sallah amma dai bincike ya nuna cewa masu yin sun fi wadanda ba su yi yawa,” inji malamin.