✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

As samu gibin N5.33trn a kasafin 2022 —Ministar Kudi

Najeriya ta samu gibin tiriliyan N5.33 daga abin da ta yi hasashen samu a cikin wata takwas na shekarar 2022 da muke ciki.

Najeriya ta samu gibin tiriliyan N5.33 daga kudaden da ta yi hasashen samu a cikin wata takwas na shekarar 2022 da muke ciki. 

Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed ta ce, gibin ya kai kashi 34 cikin 100 na kudaden shigar da gwamantin ta yi hasashen samu.

Ta kara da cewa, “Bashin da aka ci zuwa watan Agusta ya kai tiriliyan N1.26 sannan gibin da aka samu daga tiriliyan N7.53 da aka yi hasashe ya kai tiriliyan N5.53 a watan Agusta, kuma ya haura abin da aka yi hasashe da biliyan N430.82.”

Ministar, wadda take karin haske kan kasafin 2023 ta ce zuwa watan Agusta, gwamnati ta samu kudaden shiga tiriliyan N4.23trn, wanda shi ne kashi 64 cikin 10o na tiriliyan N6.65 da ta yi hasashen samu.

Gwamanti ta kuma samu biliyan N395.06 daga bangaren mai sai kuma tiriliyan N1.549 daga bangarorin da ba na mi ba.

An samu harajin kamfanoni na biliyan N826.27 da kuma biliyan N210.36 na harajni sayen kayayyaki.

Hukumar Kwastam kuma ta tara biliyan N102.51bn na kudin fito da haraji, sai wasu nau’ikan haraji na tiriliyan N2.19.

Kudaden da aka kashe sun kai tiriliyan N17.32, daga tiriliyan N11.55 zuwa karshen watan Agusta.

Ta ce, abin da aka kashe zuwa karshen watan Agusta shi ne tiriliyan N9.56 sannan an bai wa hukuomin gwamanti biliyan N1.78b domin gudanar da manyan ayyuka.