Rahotannin da ke fitowa sun nuna maiyiwuwa kulob din Arsenal ya maye gurbin kulob din Manchester City a gasar zakarun kulob na Turai (Champions League).
Hukumar shirya kwallon kafa a Nahiyar Turai (UEFA) ta ce ta fara binciken kulob din Man City ne game da yadda ya kashe kudadensa a kakar wasa ta bana, kuma idan aka samu kulob din da laifi za a iya dage shi daga shiga gasar zakarun kulob na turai.
Don haka idan aka dage City daga shiga gasar, Arsenal da ta gama a matsayi na 5 a gasar firimiya ce za ta maye gurbin City a kungiyoyi hudun da za su wakilci Ingila a yayin gasar a kaka mai zuwa.
Rahoton da kafar watsa labarai ta The UK Mirror da ake wallafawa a Ingila ta kalato ta ce tuni UEFA ta kafa kwamitin bincike a ranar Talatar da ta wuce don gano yadda kulob din City ya kashe kudadensa wajen tafiyar da harkokin wasanni a bana, kuma muddin aka samu kulob din da laifi akwai yiwuwar a dage shi daga shiga kowace irin gasa da hukumar ta shirya ciki har da na zakarun kulob na Turai.
A bana, City ce ta lashe gasar firimiyar Ingila da hakan ya ba ta damar shiga gasar zakarun kulob na turai a kaka mai zuwa.