✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Arsenal ta yi rashin nasara a Emirates

Da wannan sakamakon Brighton mai kwantan wasa biyu ta hada maki 58 tana ta shida.

Arsenal ta yi rashin nasara a Emirates da ci 3-0 a hannun Brighton a wasan mako na 36 a gasar Premier League ranar Lahadi.

Brighton ta fara cin kwallo bayan da aka koma zagaye na biyu ta hannun Julio Enciso, sannan Deniz Undav ya zura na biyu saura minti hudu a tashi wasan.

Daf da alkalin wasa zai tashi karawar Pervis Estupinan ya ci wa Brighton kwallo na uku, kenan ta hada maki ukun da take bukata.

Da wannan sakamakon Brighton mai kwantan wasa biyu ta hada maki 58 tana ta shida a teburin Premier League.

Arsenal kuwa tana mataki na biyu da tazarar maki hudu tsakaninta da Manchester City mai kwantan wasa, wadda ke neman maki uku nan gaba ta lashe kofin bana.

Saura wasa biyu ya rage wa Arsenal, kuma idan ta ci dukka za ta hada 87, bayan da tuni City keda 85, wadda za ta kara da Chelsea a Etihad, sannan ta je Brighton, sai Brentford ta karbi bakuncin City.

Wasannin da ke gaban Arsenal guda biyu:

Premier League Asabar 20 ga watan Mayu

Nottingham Forest da Arsenal

Premier League Lahadi 28 ga watan Mayu

Arsenal da Wolves