✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Arsenal ta tankade Fulham, United da Southampton sun gagari juna

United ta yi kurman duro da Southampton a Old Trafford.

Arsenal ta doke Fulham 3-0 a wasan mako na 27 a gasar Firimiyar Ingila ranar Lahadi a Craven Cotage.

Arsenal ta fara cin kwallo ta hannun ta hannun Gabriel Magalhaes aminti na 21 da fara wasa, sannan minti biyar tsakani ta kara na biyu ta hannun Gabriel Martinelli.

Daf da za a yi hutu ne Gunners ta kara na uku ta hannun kyaftin dinta, Martin Odegaard.

Ranar 27 ga watan Agustan 2022, Arsenal ta doke Fulham 2-1 a Emirates a wasan farko a babbar gasar tamaula ta Ingila da suka buga a bana.

Arsenal za ta kara a wasan gaba da Sporting a Emirates a fafatawa ta biyu a ’yan 16 a Europa League.

‘Yan wasan Arsenal suna murna a Craven Cottage

Ranar 9 ga watan Maris Gunners ta tashi 2-2 a gidan Sporting a wasan farko a gasar ta Europa ta kakar nan.

Daga nan kuma Arsenal za ta karbi bakuncin Crystal Palace a Firimiyar Ingila a wasan mako na 28 ranar 19 ga watan Maris.

Ita kuwa Fulham za ta fafata da Manchester United a daf da na kusa da na karshe a FA Cup ranar 19 ga watan Maris.

United ta yi kurman duro da Southampton 

Manchester United ta tashi 0-0 da Southampton a wasan mako na 27 a gasar Firimiyar Ingila a Old Trafford.

United ta karasa karawar da ’yan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Casemiro jan kati, karo na biyu da aka kore shi a Firimiyar Ingila.

Da wannan sakamakon United ta ci gaba da zama a mataki na uku a teburin Firimiyar da maki 50, Tottenham ce ta hudu mai maki 48.

Kafin wannan wasan United ta ci kwallo sama da biyu a wasa 15 a jere a gida a karon farko a tarihi tun bayan shekara 22.

United ta zura kwallo 99 a ragar Southampton a gasar Firimiyar Ingila, amma ta kasa ci a ranar Lahadi domin cike na 100 ko fiye da haka.

Marcus Rashford ya barar da damar yin kan-kan-kan da Wayne Rooney a tarihin cin kwallo a wasa takwas a jere a Premier a Old Trafford.

Rooney ya yi wannan bajintar tsakanin Disambar 2009 zuwa Maris din 2010.

Bruno Fernandes ya ci kwallo 99 a tarihin buga tamaula, amma bai samu cin Southampton ba, wanda ya ci uku da bayar da uku a wasa shida baya a wasa da kungiyar.

Ranar 16 ga watan Maris United za ta ziyarci Real Betis, domin buga wasa na biyu na ’yan 16 a Europa League, bayan da United ta ci 4-1 a wasan farko.

Daga nan United za ta karbi bakuncin Fulham a daf da na kusa da na karshe FA Cup ranar 19 ga watan Maris.

%d bloggers like this: