A ranar Laraba Arsenal ta tabbatar da daukar dan wasan tsakiya na Real Madrid, Martin Ødegaard a matsayin dan wasanta na dindindin.
Kungiyoyin biyu sun cimma yarjeniniyar sayen Ødegaard kan kudi €40m.
- NIHORT ta horar da manoman tumatur a Arewa Maso Gabas
- An yi harbe-harbe da kone-kone kan sauke sarakuna a Taraba
Ødegaard, ya kulla yarjejeniya da Arsenal har zuwa karshen kakar wasannni ta 2026.
Tun a farkon makon nan ne aka fara yada rahotannin cewa tafiyar Ødegaard zaman dindindin Arsenal daga Real Madrid za ta tabbata.
Dan wasan na tsakiya mai shekara 22 na kasar Norway bai yi atisaye da manyan ‘yan wasan Real Madrid ba ranar Talata, a cewar Jaridar The Athletic ta Sfinaya.
Arsenal ta jima tana son daukar Ødegaard na dindin bana wucin-gadi ba, tun bayan da ya kammala zaman aro a kungiyar.
Martin Ødegaard, ya shafe shekaru yana taka leda a matsayin wasan aro, inda a baya-bayan nan ya buga wa kungiyar Real Sociedad da Arsenal wasanni a matsayin aro.