✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Arsenal ta sayi dan shekara 18 daga Brazil

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da ke Ingila ta bayar da sanarwar kulla yarjejeniya da wani matsahi dan shekara 18 mai suna Gabreil Martinelli dan…

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da ke Ingila ta bayar da sanarwar kulla yarjejeniya da wani matsahi dan shekara 18 mai suna Gabreil Martinelli dan asalin Brazil.

Kulob din ne ya sanar da haka a ranar Talatar da ta wuce a shafin sadawarsa.

Gabreil Martinelli yana buga wa kulob din Ituano Futebol Clube da ke Brazil ne sai dai ba a bayyana takamaiman kudin da Arsenal ta sayo shi daga can ba.

Rahotanni sun nuna dan kwallon yana wasa a gaba ne kuma kulob din Arsenal ya saye shi ne bayan yunkurin da ya yi na saye Wilfred Zaha daga kulob din Crystal Palace na Ingila amma abin ya ci tura.

A tattaunawar da aka yi da Gabreil ya bayyana farin cikinsa game da damar da ya samu ta buga wa kulob din Arsenal kwallo, inda ya ce “Yanzu mafarkina ya zama gaskiya,” ganin ya koma daya daga cikin manyan kulob da ake ji da su a Nahiyar Turai.