✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Arsenal ta saye dan wasan West Ham Declan Rice

Sau biyu West Ham tana yin watsi da tayin Arsenal kan Rice.

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta bayyana cewa ta kammala ɗaukar ɗan wasa Declan Rice daga West Ham kan kudi fan miliyan 105.

Fan miliyan 100 ne gundarin kudin yayin da fan miliyan biyar na tsarabe-tsarabe ne kamar yadda Goal ta yi bayani.

Sanarwar da Arsenal ta bayar ta biyo bayan wani sako da Rice mai shekara 24 ya wallafa, inda ya bayyana wa magoya bayan West Ham cewa matakin da ya dauka na barin kungiyar abu ne mai matukar wahala.

Dan wasan mai buga tsakiya shi ne na uku cikin manyan yan wasan da Arsenal ta saya tun bayan bude kasuwar musayar yan wasa da ke ci yanzu haka.

Bayan dan wasa Kai Haverts da kungiyar ta dauko daga Chelsea da kuma Jurrien Timber daga Ajax.

Rice ya ci kwallo 15 a wasanni 245 da ya buga wa West Ham tun bayan zuwan sa kungiyar lokacin da yake da shekara 15 bayan tahowarsa daga kungiyar horaswa ta Chelsea.

Tun farko, sau biyu West Ham tana yin watsi da tayin Arsenal kan Rice ganin cewa kudin da yArsenal ta taya bai kai farashin fan miliyan 100 da West Ham ta dora kan dan wasan ba.

A baya Manchester City ta janye bayan da ta taya dan wasan fan miliyan 90 ba tare da West Ham ta sakar mata ba.