✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Arsenal ta fara yunkurin maye gurbin Sanchez

Rahotannin da ke fitowa sun nuna kulob din Arsenal da ke Ingila ya fara yunkurin saye dan kwallon kulob din Monaco na Faransa Thomas Lemar…

Rahotannin da ke fitowa sun nuna kulob din Arsenal da ke Ingila ya fara yunkurin saye dan kwallon kulob din Monaco na Faransa Thomas Lemar kafin karshen wannan watan don ya maye gurbin Aledis Sanchez da ke yunkurin komawa kulob din Manchester City.

Kocin Arsenal Arsene Wenger wanda a baya ya nuna da wuya ya sayar da Sanchez, yanzu ya yi amai ya lashe ne ganin yadda idan bai sayar da Sanchez a wannan wata ba, to zai tashi ne a tutar babu a karhen kakar wasa ta bana wato daga ranar 1 ga watan Yulin bana.

Tuni kocin Manchester City Pep Guardiola ya nuna sha’awarsa a kan Aledis Sanchez kuma akwai yiwuwar ya taya shi a kan Fam Miliyan 30.

Da zarar kulob din Arsenal ya sayar da Sanchez ana ganin zai yi gaggawar maye gurbinsa ne da Thomas Lemar.