✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Arsenal ta fara yunkurin maye gurbin Arsene Wenger

Rahotanni da ke fitowa daga Ingila sun nuna kulob din Arsenal ya fara tunanin maye gurbin kocinsa na yanzu Arsene Wenger a karshen kakar wasa…

Rahotanni da ke fitowa daga Ingila sun nuna kulob din Arsenal ya fara tunanin maye gurbin kocinsa na yanzu Arsene Wenger a karshen kakar wasa ta bana.

Kulob din ya fara wannan yunkuri ne bayan kulob din Manchester City ya lallasa na Arsenal da ci 3-0 a kofin Carabao a ranar Lahadin da ta wuce da hakan ta sa mahukunta kulob din suka fara yunkurin rabuwa da shi.

A bara ne kulob din ya sabunta kwantaragin Wenger da shekara biyu bayan ya yi kokarin lashe kofin kalubale (FA) amma a bana sai kulob din ya samu koma-baya.

A halin yanzu kulob din Arsenal yana sa rai ne a kofin Europa kuma akwai yiwuwar idan ya yi sake to za a iya yi masa sakiyar da babu ruwa a kakar wasa ta bana inda zai tashi hannu rabbana.

Sai dai ana rade-radin idan kulob din ya kori Wenger to zai maye gurbinsa ne da tsohon kocin Liberpool Brenden Rodgers da yanzu haka yake horar da kulob din Celtic.

&nbsp