✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Arsenal ta doke Manchester United a Emirates

Arsenal na ci gaba da jan ragamar teburin Firimiyar Ingila da maki 50 daga wasa 19.

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta doke Manchester United da ci 3 da 2 a wasan hamayya da suka buga a filin wasa na Emirates da ke Landan.

Dan wasan gaban Manchester United, Marcus Rashford ne ya fara zura kwallo a minti 17, amma a minti na 23 dan wasan gaban Arsenal, Nkeitah ya farke kwallon.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Bukayo Saka ya saka Arsenal a gaba, inda ya zura mata kwallo ta biyu a minti na 53, sai dai Martinez ya sake farke wa Manchester kwallon a minti na 59.

An kai ruwa rana a wasan inda Arsenal ta dinga kai munanan hare-hare kafin daga bisani dan wasanta, Nkeitah ya sake zura kwallo a minti 90, kwallon da ta raba gardama a wasan.

A halin yanzu dai Arsenal na ci gaba da jan ragama a teburin Firimiyar Ingila da maki 50 cikin wasanni 19 da ta buga, yayin da Manchester City ke biye mata a baya da maki 45 a wasanni 20.