✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Arsenal ta dauki Martin Odegaard a matsayin aro

Dan wasan zai ci gaba da zama a Arsenal har zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta dauki dan wasan Real Madrid Martin Odegaard a matsayin aro har zuwa karshen kakar wasa ta 2021.

Arsenal ta sanar da daukar dan wasan tsakiyar ne a ranar Laraba a shafinta na intanet.

Odegaard ya yanke hukuncin barin Real Madrid ne saboda rashin samun dama daga kocin kungiyar, Zinedine Zidane.

Bayan samun rashin nasarar Real Madrid a gasar Supercopa De Espana, dan wasan ya sanar da masu ruwa da tsaki na kungiyar kudurinsa na barin ta.

Sai dai Arsenal ta amince da daukan dan wasan, dan asalin kasar Norway, a matsayin aro bayan nuna sha’awa da kocinta, Mikel Arteta ya nuna.

Wannan shi ne karo na biyu da dan wasan yake barin Real Madrid a matsayin aro, bayan da ya gaza samun ishasshiyar dama.