Shugaban kamfanin Spotify ya ce masu kungiyar kwallon kafa ta Arsenal sun yi watsi da tayinsa na sayen kulob din, amma har yanzu yana kan bakarsa.
Daya daga cikin wadanda suka kafa Spotify, Daniel Ek, ya bayyana a ranar Asabar cewa Kroenke Sports, masu kulob din Arsenal, sun ki amincewa da tayin da ya yi na sayen kungiyar da ke buga Gasar Firimiyar kasar Ingila.
- Iheanacho da Ndidi sun taimaki Leicester ta lashe kofin Gasar FA
- Buhari zai tafi Paris halartar taron kasashen Afrika
“A wannan makon an gabatar da tayin ga Josh Kroenke da masu kula da bankinsu, wanda ya hada da mallakar magoya baya, wakilci a hukumar da kuma kaso mai tsoka ga magoya bayan,” inji Ek.
Sanarwar da ya fitar a shafinsa na Twitter, attajirin dan kasar Sweden din ya ce Kroenke Sports, sun bayyana masa cewa Arsenal ba ta sayarwa ba ce.
Masu Arsenal, “Sun amsa cewa ba sa bukatar kudin. Amma ina da sha’awar idan suka sauya shawara kan lamarin,” inji shi.