Ministan Birnin Tarayya, Ezenwo Nyesom Wike ya ce ko na’urar bibiyar wayoyi jami’an tsaro ba su da da ita, da na aro suke amfani idan bukatar hakan ta taso.
Wike ya sanar da cewa rashin kayan bibiyar sawun miyagun ya taimaka wajen karuwar ayykansu, amma da zarar an sayo kayan aikin, labari zai sauya.
Ministan ya ce don haka Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin gaggawa na yin odar kayan bibiyar sawun ’yan bindiga da sauran ’yan ta’adda da suka addabi Najeriya.
A cewarsa, “akwai kayan aiki da dama da jami’an tsaro ba su da su, kamar motoci da sauransu; hatta na’urar bibiyar wayoyi ba su da ita, don haka idan wani abu ya faru sai dai su je su nema a Ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa kan Harkokin Tsaro.”
“Amma da wannan umarnin da shugaban kasa ya bayar mun gano duk irin abubuwan da kowace hukumar tsaro tsaro take bukata kuma za mu samar mata da su.”
Wike ya sanar da haka ne a ranar Litinin yana mai karawa da cewa ’yan leken asirin ’yan bindiga da aka kama suna ba da hadin kai a binciken da ake gudanarwa.
A cewarsa, bayanan da suka bayar ne suka kai ga cafke wasu masu garkuwa da mutane tara a karshen mako da kuma nasarar da jami’an tsaro suka samu wajen dakile wasu hare-hare.
Wannan cigaba dai na zuwa ne a daidai lokacin da hare-haren ta’addancin masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa ke karuwa a Abuja.
A cewar Wike, kasancewar hukumar gudanarwar Abuja ba za ta iya kafa hukumar tsaro mai zaman kanta ba, amma za ta kafa rundunar hadin gwiwa ta kuma samar musu da kayan aiki domin a kai ga nasara a bangaren tsaro.