✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Armeniya da Azerbaijan za su yi musayar fursunoni

Rayuka fiye da dari biyu ne suka salwanta a rikicin baya-bayan nan a tsakanin makwabtan biyu.

Kasashen Armeniya da Azerbaijan za su yi musayar fursunoni kimanin 17 a matakin farko na son ganin sun shawo kan rigingimun da suka hanasu zaman lafiya.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ne ya shiga tsakani don ganin an yi sulhu a tsakanin Armeniya da makwabciyarta Azerbaijan da suka jima suna fada da juna.

Shi ne dai matakin farko da ke nuna an kama hanyar sulhunta rikicin, bangarorin biyu sun amince su yi musayar fursunonin.

Bayanai sun ce an cimma matsayar bayan wata tattaunawa da Mista Blinken ya yi ta wayar tarho da Shugaba Ilham Aliyev na Azerbaijan a ranar Litinin.

Blinken ya kuma bayyana aniyar Amurka na ba su goyon baya wurin warware muhimman batutuwan da suka haifar da sabanin, musamman bayar da damar hawa teburin sulhu kan yankin nan na Nagorno-Karabakh da suka jima suna jayayya a kai.

Rayuka fiye da dari biyu ne suka salwanta a rikicin baya-bayan nan a tsakanin makwabtan biyu.

%d bloggers like this: