Gamayyar Al’ummar Arewa (CNG) ta bayyana yanke kauna daga kasassabar da ta ce Gwamantin Tarayya ta yi bayan Boko Haram ta kashe manoma a Zabarmari, Jihar Borno.
CNG ta ce furucin jami’an gwamnatin bayan fushin da jama’a suka nuna kan kisan kiyashin da aka yi wa manoman shi ne makurar wauta da rashin damuwa da rayuwar al’umma.
“Tantagaryar shiririta, abin kyama, abin kunya da Allah-wadai ne irin kalaman da mashawartansa da ministocinsa suka yi game da mawuyacin halin da jama’ar Arewa ke ciki da ke bukatar daukar matakan gaggawa.
“Kashe-kashen na barazanar kawo yunwa tare da rusa kokarin samar da abinci musamman a Arewa inda masu satar mutane da ’yan bindiga ke hana manoma sakat”, inji CNG.
“Kisan Zabarmari ya yi fice ne saboda yawan mutanen da aka kashe a lokaci daya a kuma wuri guda, amma ya kamata duniya ta sani cewa ’yan ta’adda na yawan yin kisan kiyashi da satar mutanne musamman a Arewacin Najeriya”, inji sanarwar da kakakin kungiyar, Abdul-Azeez Suleiman ya fitar.
Kungiyar ta ce jazaman ne al’ummar Arewa su kare kansu, tunda Gwamnatin Buhari ta gaza, duk da rantsuwar da ya yi na kare rayukan ’yan Najeriya.
“Don haka CNG za ta gudanar da nabban taro kan tsaron Arewa daga 14 zuwa 15 ga Disamba, 2020 a Kaduna inda masana tsaro, sarakuna, malaman addini, kungiyoyi, ’yan kasuwa, matasa, mata da wakilan gwamnati za su tattauna.
“Taron zai lalubo hanyoyin samar da hadin kai a matakan jihohi da al’ummomi domin daukar matakan tsaro na bai-daya kuma a al’ummance tare da inganta hadin kai ta fuskar tsaro da samar da bayanai.
CNG ta yi kira da “a bincika a hukunta masu azurta kansu da kasuwanci a yaki da Boko Haram da kuma ikirarin nasarar da ake ta yi a yakin da duniya ke ganin koma baya a ciki.
“Muna Allahwadai da dukkanin nau’ikan manyan laifi da duk masu tunzurawa a aikata su a ko a karya doka a ko’ina a Najeriya”, inji ta.
Katobarar Gwamnatin Buhari
Kungiyar ta ce kololuwar wauta ce zargin da kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu ya yi wa manoman da aka kashe cewa sun karya dokar sojoji; Ministan Yada Labarai Lai Mohammed da ya ce akwai siyasa a fushin da aka nuna kan kisan gillar; da uwa uba hasashen da Shugaban Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Tukur Buratai ya yi cewa za a shekara 20 nan gaba ana fama da matsalar tsaro a Najeriya.
Kungiyar ta ce lafuzzan jami’an gwamnatin sun karyata ikirarin Gwamnatin Buhari na cewa sojoji sun galabaitar da Boko Haram sun kuma fatattaki kungiyar daga garuruwan yankin Arewa maso Gabas.
Furucin, a cewar kungiyar, sun tabbatar da zargin da ake yi wa masu hannu a yaki da Boko Haram sun mayar da shi hanyar samun kudi.
“Shirun Buhari a kan kalaman ya nuna Gwamanti ba ta damu ba da kashe-kashen da ake yi a Borno, kuma Fadar Shugaban Kasa ta yi watsi da kiraye-kiraye da shawarwari da ake ba ta kan hanyoyin inganta sha’anin tsaro da sanya shugabannin soji yin aikinsu yadda ya kamata.
“Muna jaddada matsayinmu cewa Buhari da Gwamantinsa sun gaza a babban aikinsu na kare ’yan Najeriya.
“Muna kiran daukacin ’yan Arewa su matsa wa gwamnoni da Gwamantin Tarayya su tababtar an sauya fasalin tsarin tsaro ta yadda za a magance matsalolin satar mutane, ’yan bindiga da sauran matsalolin da ke kawo wa yankin koma-baya.
Matakin da za a dauka
Kungiyar ta ce ayyukan ’yan ta’adda, masu satar mutane, ’yan bindigya, ’yan fashi, kashe-kashen da kone-kone ba gaira ba dalili da suka zama ruwan dare a Arewa sun sa yankin ba shi zabi face ya tashi ya kare kansa, “tunda shugabannin da muke da su ba masu jin kushe ko daukar shawara ba ne”.
“Kauracewar da Shugaban Kasa da gwamantinsa suka yi daga babban nauyin da ya rataya a wuyansu na samar da tsaro a dukkannin sassan kasar nan shi ne babban hujjar yunkurin tsare kanmu”, inji ta.
“A lokacin da ISIS ta fara mamaye yankin Kurdistan na kasar Iraki, ’yan sa-kan Kurdawa na Peshmerga ba yanke kauna suka yi, suka zura ido suna jiran dakarun gwamnatin kasar su kare su ba.
“Haduwa suka yi suka kafa rundunar mayakan sa-kai wadda mahukuntan yankin suka dau nauyi suka kuma ba ta cikakkiyar goyon baya don kare yankin kuma ta samu nasara a kan ISIS.
“Hakan na iya yiwuwa a Arewa idan ’yan yankin suka hada kai, suka tara isassun kudade, suka jagoranci matasa don kawo karshen hare-haren, karya ’yan ta’addan da kuma samar da hadin kan yankin”, inji ta.