✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Arewa ba za ta ci gaba ba sai da tsayayyen jagora – Sheikh Khalil

Shugaban Majalisar Malamai ta Kasa reshen Jihar Kano Sheikh Ibrahim Khalil ya bayyana cewa yankin Arewa ba zai taba samun tagomashi ba, ba tare da…

Shugaban Majalisar Malamai ta Kasa reshen Jihar Kano Sheikh Ibrahim Khalil ya bayyana cewa yankin Arewa ba zai taba samun tagomashi ba, ba tare da samun tsayayyen jagora ba.

Sheikh Ibrahim Khalil ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a Kano. Ya ce a mafi yawan lokaci, rashin tsayayyen jagora a Arewa ne ya sanya idan kowa ya debo shararsa sai ya juye a kan ’yan Arewa. “Hakan ya sa idan aka tashi magana sai a ce ’yan Arewa ne masu almajirai, su ne masu mutuwar aure, su ne suka fi talauci, su ne suka… bayan kuma kowane bangare yana da tasa matsalar amma ba a fadin nasa sai na Arewa. Wannan zai ci gaba da faruwa har sai mun yarda mun tsayar da jagora guda daya daga cikinmu. Hakan shi zai ba mu karfi domin a duniya idan ba ka da karfi ba wanda zai karbe ka ballanatana ya saurare ka,” inji shi.

Malamin ya yi kira ga ’yan Arewa su ajiye bambance-bambancen da ke tsakaninsu, su hada kai tare da amincewa da wani jajirtacce a cikinsu don ya zama jagoransu, wanda zai zama yana magana da muryarsu.

“A rayuwa ba zai taba yiyuwa ra’ayi ya zama daya ba, akwai kungiyoyi da dama ba zai yiwu a ce su narke su zama abu daya ba. Abin da ake bukata shi ne a samu wata mahada da za ta rika hada su yadda za a samu fahimtar juna, yadda za a rika tattaunawa idan wani abu ya taso a zauna tare a nemar wa kai mafita. Amma ba kowa ya zauna yana yin gaban kansa shi kadai ba. Don haka dole duk da bambancin ra’ayi ko siyasa a samu wani jagora wanda zai riki yankin Arewa. Mun san ba zai yiwu a ce kowa ya amince da mutum guda ba, amma akan ajiye bambanci don samun mafita,” inji malamin.

Ya ce “Idan mun duba a kasar nan, Yarbawa suna da bambance-bambace a tsakaninsu amma duk da haka sun hadu sun riki Tinubu a matsayin jagoransu.”

Malamin ya ce duk wanda zai zama jagoran al’umma dole sai ya kasance jarumi mara tsoro, jajirtace mai iya mu’mala da mutane. Ya ce, “Mun san dan Adam tara yake bai cika goma ba ko kuma mu ce yayin da wani yake ganin wane a matsayin marar laifi; ba haka wani yake kallon lamarin ba. Amma abin da ake son aiki da shi shi ne mutumin da zai zama jagoran ya samu amincewa da yardar kaso mai yawa na mutanensa. Misali a nan, mutum zai iya zuwa ya ce mu dauki Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso domin shi ne ake gani a matsayin gogaggen dan siyasa, jajirtacce haka kuma jarumi. A duk Arewa babu wanda yake da tsararriyar jama’a cikakkun mabiya kamar tasa, babu mai himma amma duk da wadannan abubuwa da muka lissafo sai ka ga wani ya taso ya ce bai yarda ba. To a nan bai kamata mutum ya ki nuna amincewarsa ba matukar ya san cewa Kwankwason misali zai iya zama jagoran al’umma.”

“Abin da ya kamata mutum ya yi ko da ba ya ra’yin Kwankwaso shi ne sai ya ki shiga kungiyar Kwankwasiyya amma ya yarda ya aminta cewa Kwankwaso zai jagorance shi a matsayinsa na dan Arewa kawai. Ba zai yiywu a ce sai kowa ya amince da mutumin da aka tsayar kafin ya zama jagora ba, wanann ba zai taba yiyuwa ba;” inji malamin.