Sarkin Fulanin Jihar Edo, Alhaji Ardo Muhammadu Usman (Sosal) ya buƙaci al’ummar Fulani makiyaya da suke jihar da jihohin da suke maƙwabtaka da jihar su tabbatar da hadin kai a tsakaninsu domin samun zaman lafiya a jihar.
Sarkin Fulanin ya bayyana haka ne a Benin fadar Jihar Edo lokacin da yake tattaunawa da Aminiya.
Ya ce kiran ya zama wajibi don ganin al’ummar Fulani makiyaya mazauna jihar da jihohin da suke kewaye da jiharsun fahimci juna a tsakaninsu domin ta wannan hanyar ce za su tabbatar da kome na tafiya yadda ake buƙata.
Sarkin Fulani Ardo Muhammadu Usman (Sosal) ya ƙara da cewa “Gaba daya ci gaban al’umma ya dogara ne a kan zaman lafiya da ƙaunar juna.
“Saboda haka ina shawartar ’yan uwana a’lummar Fulani makiyaya mazauna Jihar Edo a kan hadin kai da bin doka da oda kuma su guji tayar da fitina ko ɓarnar amfanin gona.
“Su kuma takwarorina ardodin Fulani su riƙa tuntuɓar juna a kan abubuwa da suka shafi zaman lafiyar wadanda suke jagoranta da wayar musu da kai kan yadda za su tafiyar da rayuwarsu cikin jama’a.
“Kuma su himmatu kan karɓar katin zaɓe domin da shi ne za su iya zaɓar wanda suke so a zaɓen jihar da ke tafe.”