Jam’iyyar APC ta yi Allah dai da tsamin dangartakar da ke tsakanin Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya da tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Danjuma Goje.
A ranar Asabar ce jam’iyyar ta yi tir da wannan lamari yayin wani taron manema labarai da shugabanninta suka gudanar.
A kan haka ne sshugabannin jam’iyyar ke kira ga gwamna Inuwa Yahaya da Sanata Danjuma Goje da su sasanta rikicin da ke tsakaninsu.
Sun yi kiran ne kwanaki kadan bayan an yi hatsaniya a jihar ta Gombe tsakanin bangaren gwamnan da na Sanatan yayin da Goje ya kai ziyara jihar da ta kai an hana shi shiga.
Hatsaniyar dai a yanzu kowane bangare ya zargi daya bangaren da haddasawa, ta yi sanadin mutuwar akalla mutum biyar.
Shi kuwa Jakada Moses Kyari, mai magana da yawun jam’iyyar yayin bayyana matsayarsu, ya ce rikicin Goje ne ya jawo shi kuma ya yi sanadiyar rasa rayuka 5 da asarar dukiyoyi ta miliyoyin naira.
Moses ya yi kira ga jami’an tsaro da su duba lamarin su gano wadanda suka kitsa rikicin su fuskanci hukunci komai girman mukamin wanda aka samu da laifi.
Moses ya kuma nemi Sanata Danjuma Goje da ya fito fili a kafafen yada labarai ya nemi gafarar jam’iyyar APC da al’ummar jihar bisa rayuka da dukiyoyi da aka rasa a dalilinsa.
A karshe jam’iyyar APC ta nesanta kanta daga wannan rikicin tana kuma yin Allah wadai da shi.
Ana iya tuna cewa, Juma’ar da ta gabata ce Sanata Danjuma Goje ta zargi babban dogarin gwamnan Jihar da kuma shugaban Matasan Jam’iyyar na Jihar Gombe, Kawu Lero da Direban gwamnan da hasa da ’yan daba suka tare masa hanya bayan sauka a filin jirgin sama na Lawanti yayin da kai ziyara jihar.
Ana tsakar haka ne hatsaniya ta kaure tsakanin bangarorin biyu da ta kai ga an yi kone-kone wanda ya janyo asarar rayuka da dukiyoyin al’umma.