Jam’iyyar APC mai mulki ta nemi jam’iyyar adawa ta PDP da ta rufe hedikwatarta matukar ba za ta iya biyan ma’aikatanta hakkinsu ba.
Hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da Mataimakin Sakataren Yada Labaran APC, Yekini Nabena ya fitar.
- APC na amfani da ’yan ta’adda wurin magudi – Agboola
- Buhari zai kai Najeriya ya baro da cin bashi —PDP
- ‘Yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban APC a Zamfara
- Zanga-zanga: ‘Yan PDP na neman a kori Maibasira
“Kwanan nan sakatariyar jam’iyyar ta kori wani mutum da ke aiki da ita.
“Rashin adalci jam’iyyar ya sa ta kori kaso 50 na ma’aikatanta”, inji shi.
Jam’iyyar APC ta ce jam’iyyar da ba ta biyan ma’aikata albashi amma tana ba su damar yin tawaye a cikin azaba, bai kamata a zabe ta a kan mulki ba.
Wasu daga cikin ma’aikatan da aka sallama tuni sun maka PDP a Kotun Sasanta Rikicin Ma’aikata ta Kasa, domin neman hakkinsu.
APC ta kara da cewa yana daga cikin zalunci ka ki biyan ma’aikaci hakkinsa bayan ya maka aiki.
Ta kara da cewa babu abinda PDP ta iya face farfaganda.
Rahotanni sun bayyana cewa tun bayan rasa mulki da jam’iyyar ta yi, ta kasa biyan ma’aikatanta wasu alawus-alawus dinsu.
Da yake mayar da martani a wata hira ta wayar tarho da wakilinmu, Sakataren Yada Labaran PDP na Kasa, Kola Ologbondiyan ya ce, “ba abin da (APC) ta ke yi face hauragiya”.