✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta roki jami’an tsaro su binciko wanda suka kashe shugabanta

’Yan daba sun kai mishi hari ne a wurin sabunda rajistar ’yan jam'iyyar APC

Jam’iyyar APC reshen Jihar Binuwai ta roki hukumomin tsaro da su binciko masu hannu a kashe shugabanta na Mazabar Gboko ta Kudu, Tersoo Ahu, da wasu bata gari suka yi.

Sakataren jam’iyyar na Jihar, James Ornguga ne ya yi kiran a lokacin da yake ganawa da Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN), a ranar Lahadi a Makurdi.

“Mun yi tir da kashe Shugaban mazabarmu na  jam’iyyar APC mai son zaman lafiya.

“Duk wadanda suka aikata hakan su sani cewa jam’iyya ba zata kyale ba,” a cewar Ornguga.

Ya kara da cewa jam’iyyar tana rokan jami’an tsaro da su zurfafa binciken gano masu hannu a kisan.

Al’amarin ya faru ne a ranar Lahadi, yayin da ’yan jam’iyyar APC ke sabunta rajistarsu, inda wasu ’yan daba sukai kai musu harin da ya yi sanadin mutuwar Mista Tersoo.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Binuwai ta tabbatar da rasuwar Tersoo Ahu sakamakon farmakin da ’yan dabar suka kai wajen sabunta rajistar jam’iyyar.