Jam’iyyar APC reshen Jihar Binuwai ta roki hukumomin tsaro da su binciko masu hannu a kashe shugabanta na Mazabar Gboko ta Kudu, Tersoo Ahu, da wasu bata gari suka yi.
Sakataren jam’iyyar na Jihar, James Ornguga ne ya yi kiran a lokacin da yake ganawa da Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN), a ranar Lahadi a Makurdi.
- Karamin yaro ya salwantar da N1.2m a wayar uwarsa
- Za mu shirya mukabala tsakanin Abduljabbar da Malamai — Ganduje
- El-Rufai ga Gumi: Ba za mu yi sulhu da ’yan bindiga ba
- Zulum ya gwangwaje mutanen Gwoza da tallafin kayan abinci da kudade
“Mun yi tir da kashe Shugaban mazabarmu na jam’iyyar APC mai son zaman lafiya.
“Duk wadanda suka aikata hakan su sani cewa jam’iyya ba zata kyale ba,” a cewar Ornguga.
Ya kara da cewa jam’iyyar tana rokan jami’an tsaro da su zurfafa binciken gano masu hannu a kisan.
Al’amarin ya faru ne a ranar Lahadi, yayin da ’yan jam’iyyar APC ke sabunta rajistarsu, inda wasu ’yan daba sukai kai musu harin da ya yi sanadin mutuwar Mista Tersoo.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Binuwai ta tabbatar da rasuwar Tersoo Ahu sakamakon farmakin da ’yan dabar suka kai wajen sabunta rajistar jam’iyyar.