✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

APC ta lashe zaben kananan hukumomin Kano

APC ta lashe daukacin kujerun shugabannin kananan hukumomi 44 da kansiloli 484

Jam’iyyar APC ta lashe kujerun shugabannin kananan hukumomin Jihar Kano 44 gaba daya a zaben da aka gudanar a ranar Asabar.

Shugaban Hukumar Zabe ta Jihar Kano (KANSIEC), Farfesa Garba Ibrahim Sheka ya sanar da sakamakon zaben a ranar Lahadi, tare da cewa jam’iyyar APC mai mulki jihar ce kuma ta lashe daukacin kujerun Kansiloli 484 da ke Jihar.

Ya ce duk da cewa zaben ya yi fama da matsaloli a zaban, amma an samu gagarumar nasara wurin gudanar da zaben cikin lumana.

Ya yaba wa Gwamnatin Jihar bisa rashin yi wa KANSIEC katsalandan wurin shiryawa da kuma gudanar da zaben.

Aminiya ta kawo rahoto inda Gwamna Abdullahi Ganduje ke bayyana kwarin gwiwa cewa jam’iyyar APC ce za ta yi nasara a zaben shugabannin kananan hukumomi 44 da kansiloli 484 a jihar, bisa la’akari da yanayin fitowar mutane zaben a mazabarsa da ke kauyen Ganduje.