✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

APC ta lashe zaben cike gurbi a Jigawa

Dan takarar dai ya sami kuri’a 29,372, inda ya doke abokin karawarsa na PDP.

An bayyana dan takarar Jam’iyyar APC a zaben cike gurbi na dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Gwaram a Jihar Jigawa,  Alhaji Yusuf Galami a matsayin wanda ya lashe zaben.

Baturen zaben yankin, Farfesa Ahmad Shehu ne ya bayyana dan takarar a matsayin wanda ya yi nasara a zaben na ranar Asabar, bayan tattara sakamakon zaben daga rumfuna 248.

Ya ce Alhaji Yusuf ya sami kuri’a 29,372, inda ya doke abokin karawarsa, Kamilu Inuwa, na Jam’iyyar PDP, wanda ya samu kuri’a 10,047.

Farfesa Ahmad ya ce, “Kasancewar Galambi wanda ya fi sami kuri’u mafi rinjaye ya kuma cika dukkan ka’idojin da doka ta tanada, an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben,” kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, (NAN) ya ruwaito Farfesa Ahmad Shehun yana fada a safiyar Lahadi a Gwaram.