Dokta Iyorchia Ayu daga Jihar Binuwai a yankin Arewa ta Tsakiya ya zama sabon Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa ba tare da hamayya ba.
Hakan ya faru ne bayan babban taron jam’iyyar na kasa, wanda Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya jagoranci gudandar da zaben sabbin mambobin Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC) na jam’iyyar.
- Zaben PDP: An umarci daliget su yi zabe da ‘Unity List’
- 2023: Ba za mu bari a kai takara Kudu saboda son kai ba – Sule Lamido
Da yake jawabi bayan zaben, Dokta Iyorchia Ayu, ya bayyana jam’iyyar APC mai mulki a matsayin taron yuyuyu, inda ya ce, “Muna jiran su, mun kuma ba su notis din kwashe komatsanu; PDP ta dawo kuma za ta karbe mulkin kasar nan domin ta bunkasa ta.”
A cewarsa, mutane za su yi dafifin zaben PDP a zabe mai zuwa na 2023, “PDP ta dawo ne domin ta ceci Najeriya daga shiritar da APC ta shekara shida tana yi.”
Taron na PDP ya kuma zabi Ambasada Ali Umar Iliya Damagum a matsayin Mataimakin Shugaban Jam’iyya daga yankin Arewa, bayan an fafata a akwatin zabe a babban taron da aka kammala.
Fintiri ya sanar cewa Ambsada Damagum (Sakataren Tsare-tsaren taron) ya samu kuri’a 2,222 inda ya kayar da abokiyar karawarsa, tsohuwar Ministar Harkokin Mata kuma Shugabar Mata ta Jam’iyyar, Hajiya Inna Ciroma, wadda ta samu kuri’a 365.
Ambasada Taofeek Arapaja kuma ya samu nasarar zama Mataimakin Shugaban Jam’iyya daga yankin Kudu da kuri’a 2,004 bayan ya kayar da Prince Olagunsoye Oyinlola, wanda ya samu kuri’a 705.
Sabon Shugaban Matasan Jam’iyyar PDP na Kasa shi ne Muhammed Kadade Suleiman, inda ya samu 3,072 ya kayar da Usman Elkudan mai kuri’a 219.
Fintiri ya sanar cewa daliget 3,511 ne aka tantance suka kada kuri’a a zaben wanda aka samu lalatattun kuri’a 165.
– APC ba za ta iya babban taro lafiya ba —Dokta Ayu
A ci gaba da jawabinsa, sabon shugaban jam’iyyar PDP, Dokta Iyorchia Ayu, ya ce, “Mutane da dama sun yi zaton babban taron nan da muka gudanar zai ruguza PDP, to su sani cewa mafarki suke yi.”
Ya yi wa APC gugar zana da cewa, “Na yi imani waccan ba za ta iya yin babban taro ba.
“Taron jihohi ma ta kasa, inda ta wayi gari da shugabanni 92 maimakon 36; To ta yaya za su iya yin babban taro cikin nasara kamar PDP?
“Wadanda suka yanke kauna su sani cewa Najeriya kasa daya ce, wasu tsirarun mutane ne ke neman yaga ta.
“PDP na nan za ta sake dawowa ta hade kan jama’ar kasar daga kowane bangare tare da kawo cigaban kasa.”
– Zabe babu hamayya –
Sauran mambobin Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar na kasa 17 kuma sun samu nasara ne ba tare da hamayya ba, kamar yadda wakilinmu ya ga jerin sunayen sabbin shugabannin su 21 a wurin taron.
Sauran shugabannin jam’iyyar su hada:
- Sanata Samuel Anyanwu, Imo — Sakatare
- Hon. Yayari Mohamme, Gombe — Ma’aji
- Hon. Umari Bature, Sakkwato — Sakataren Tsare-tsare
- Daniel Woyengikuro, Bayelsa —Sakataren Kudi
- Farfesa Stell Effa-Attoe, Kuros Riba — Shugabar Mata
- Kamaldeen Adeyemi Ajibade (SAN), Kwara — Mashawarci kan Shari’a
- Hon. Debo Ologunagba, Ondo — Sakatare Watsa Labarai
- Okechukwu Obiechina Daniel, Anambra — Mai Bincike Kudi
- Arch. Setoji Kosheodo, Legas — Mataimakin Sakataren Jam’iyya
- Ndubuisi Eneh David, Enugu — Maitaimakin Mai Binciken Kudi
- Alhaji Ibrahim Abdullahi, Kebbi — Mataimakin Sakataren Yada Labarai
- Sanata Ighoyota Amori, Delta — Mataimakin Sakatare Tsare-tsare
- Hon. Adamu D.U Kamale, Adamawa — Mataimakin Sakataren Kudi
- Hajara Yakubu Wanka, Bauchi — Mataimakiyar Shugabaar Mata
- Timothy Osadolor, Edo — Mataimakin Shugaban Matasa
- Barisata Okechukwu Osuoha, Abia — Mataimakin Mashawarci kan Shari’a
- Hon. Abdulrahman Mohammed, Abuja — Mai Binciken Kudi.