✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta janye korar da aka yi wa Sanata Goje

APC reshen Jihar Gombe ta kori Goje kan zargin yin zagon kasa a zaben 2023

Uwar Jam’iyyar APC ta jingine korar da reshenta na Jihar Gombe ya yi wa tsohon gwamnan jihar, Sanata Danjuma Goje, kan zargin zagon kasa a zaben da ya gabata.

Sakataren Yada Labaran uwar jam’iyyar APC,  Felix Morka, ya shaida wa ‘yan jarida a Abuja cewa, jami’iyyar ta jingine hukuncin da reshenta na jihar ya dauka a kan Sanata Goje, da nufin sake nazarin batun.

Felix Morka ya ce, Kwamitin Gudanarwa na Jam’iyyar (NWC) ne zai sake nazari kan abubuwan da suka kai ga daukar matakin korar Goje a Gombe, amma har yanzu shi halastaccen dan jam’iyyar ne.

Ya ce uwar jam’iyyar ta damu saboda yawaitar matakin ladabtarwa da rassan jam’iyyar na jihohi ke dauka kan zargin mambobi da laifuka, ciki har da a lokacin zabukkan da aka kammala.

A don haka za ta dauki matakan da suka dace na yin gyara domin tabbatar da hadin kai da karin karfin jam’iyyar a dukkan matakai, musamman ganin cewa yanzu lokaci ne da ake kokarin fara sabuwar gwamnati da kafar dama.

Don haka ya umarci duk rassan jam’iyyar da su dakatar da daukar matakan ladabtarwa, har sai sun ji daga NWC.