Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, ta fidda jadawalin zaben cikin gurbi na ‘yan majalisun tarayya da suka fito daga jihohin Bayelsa, Borno, Legas, Filato, Zamfara, Kuros Riba, Imo da kuma Kogi.
Tuni dai daman Hukumar Zabe ta Kasa mai zaman kanta INEC, ta sanya 31 ga watan Oktoban 2020, a matsayin ranar da gudanar da zabukan na cike gurbi.
Cikin sanarwar da mai magana da yawun jam’iyyar APC na kasa Yekini Nabena ya fitar a ranar Talata, ya ce za a tantance ‘yan takarar a ranakun Laraba da Alhamis, inda kuma za a wallafa sunayensu da tsare-tsaren zaben a ranar juma’a.
A cewarsa, za gudanar da zaman sauraron korafin tantance ‘yan takarar a ranar 1 ga watan Satumba, yayin da za a gudanar da zaben tsayar da ‘yan takara a ranar 3 ga watan Satumba.
Haka kuma sanarwar da Mista Nabena ya fitar ta yi bayanin cewa, za a gudanar da zaman sauraron korafin zaben fidda ‘yan takara a ranar 5 ga watan Satumba.
Aminiya ta fahimci cewa, an kafa kwamitin tantance ‘yan takara da kuma kwamitin sauraron korafi a duk jiha gabanin zaben ya gudana.