Kwamitin yakin neman zaben Jam’iyyar NNPP ya ce jam’iyyar APC za ta sha wahala a zabe mai zuwa saboda yadda magoya bayanta suka daina son ta a Arewa.
Mai magana da yawun kwamitin Abdulmuminu Jibrin Kofa, ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels a ranar Litinin.
- Borno ta Tsakiya: Kotu ta soke da takarar Sanatan PDP
- Zan dora daga inda El-Rufai ya tsaya a Kaduna —Uba Sani
“Ko yaushe APC za ta yi magana za ta ce PDP ta rasa Kwankwaso, ta rasa Peter Obi, ta rasa goyon bayan G-5.
“Gaskiya ne PDP na cikin matsala, amma APC ta fi ta shiga matsala saboda kuri’a miliyan 12 da ta samu a Arewa ba za ta same su a zabe mai zuwa ba.
“Idan aka ce Kwankwaso ya fice daga PDP, tunanin da ake yi shi ne ya tafi da magoyan PDP kadai, amma kuma ai har da magoya bayan APC ya tafi,” cewar Kofa.
Ya kara da cewa yawancin magoya bayan APC a Arewa sun koma tafiyar Kwankwaso.
“Idan Kwankwaso ya samu ruwan kuri’a musamman daga Arewa Maso Yamma da kuma Kudancin kasar nan, zai lashe zaben shugaban kasa.”
A baya Abdulmuminu Jibrin Kofa, ya kasance Darakta-Janar na kungiyar magoya bayan Tinubu kafin daga bisani ya fice daga jam’iyyar.
Kofa dai ya samu matsala da gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, wanda hakan ya sanya shi ficewa daga APC.
Ya jima yana so ya sake komawa kujerarsa ta dan Majalisar Tarayya, amma takun sakar da ke tsakaninsa da Ganduje ya yi masa kaka-gida.