✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta dakatar da Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa

An dakatar da Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa Mista Damishi Barau Luka daga Jam’iyyar APC, mai mulkin jihar. Shugaban jam’iyyar Mista Stanley Buba ne ya sanar…

An dakatar da Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa Mista Damishi Barau Luka daga Jam’iyyar APC, mai mulkin jihar. Shugaban jam’iyyar Mista Stanley Buba ne ya sanar da haka ga manema labarai a sakatariyar jam’iyyar da ke Lafiya a ranar Litinin da ta gabata, inda ya ce jam’iyyar ta dakatar da Mataimakin Gwamnan ne saboda ya daina halartar tarurrukan jam’iyyar a jihar da kasa baki daya inda yake hulda da Jam’iyyar PDP. “Mataimakin Gwamnan ya sha bayyana wa manema labarai cewa manufofi da shirye-shiryen Jam’iyyar APC a jihar da kasa ba za su iya kawo ci gaba mai ma’ana ga kasar nan ba,” inji Shugaban. Ya ce jam’iyyar tana shirin korar Mataimakin Gwamnan daga jam’iyyar, inda za ta kafa kwamitin da zai gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake masa. Ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar a jihar su kasance cikin natsuwa da yin aiki tukuru don ci gaban jam’iyyar, inda ya ce jam’iyyar ba za ta yi wata-wata ba wajen hukunta duk wanda aka gano yana karya dokokinta kamar yadda ake zargin Mataimakin Gwamnan. kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin Daraktan Labarai na Mataimakin Gwamnan kan batun ya ci tura saboda ba ya a gari, kuma lambar wayarsa ba ya tafiya a lokacin da ake hada wannan rahoto.