Mako biyu kafin zaben shugaban kasa, Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta dage taronta na yakin neman zaben shugaban kasa a Jihar Kano, har sai abin da hali ya yi.
Da farko jam’iyyar ta shirya gudanar da gangamin yakin neman zaben ne a ranar Alhamis 16, ga watan Fabrairun da muke ciki, kimanin kwana 10 kafin zaben shugaban kasa ranar 25 ga wata.
- Kotu ta kori Mohammed Abacha daga takarar gwamnan Kano
- Canjin kudi zai shafi ayyukan sojoji —Monguno
Mun nemi sanin dalili, amma Festus Keyamo ya ce, “Sauye-sauye aka samu abin da aka shirya.”
Sai dai ziyarar ta Buhari — wanda ya yi alkawarin jagorantar yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu — ba ta yi armashi ba.
Jama’a ba su yi dafifin tarbarsa yadda aka saba ba a Kano, jihar da APC ke bugun tunkaho da ita da kuma tunanin samun ruwan kuri’u kamar a zabukan da suka gabata; A zabukan shugaban kasa na 2015 da 2019 APC ta samu a Kano fiye da ko’ina a fadin Najeriya.
Mutane da dama sun bayyana rashin fitowar mutane tarbar Buhari a matsayin alamar raguwar farin jininsa a Kano, a yayin da wasu ke danganta lamarin da canjin kudi da gwamnati ta yi, wanda ya sa samun tsabar kudi gagarar yawancin ’yan Najeriya.
Sai dai a wani martaninta, Fadar Shugaban Kasa, ta ce har yanzu Shugaba na nan da farin jininsa a wurin Kanawa.
Jihar Kano dai na da muhimmanci a zaben shugaban kasa, inda jihar ke kan gaba a Arewa kuma ta biyu a Najeriya wajen yawan masu katin zabe, ga shi kuma dan asalin jihar kuma tsohon gwamna, Sanata Rabiu Musa Kwankwako, ya fito takarar shugaban kasa a Jam’iyyar NNPP.