✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta dage manyan tarukanta har sai abin da hali ya yi

Hakan dai na kunshe ne a wata wasika da jam’iyyar ta aike wa INEC.

Jam’iyyar APC mai mulki ta sanar da dage manyan tarukanta tun daga matakin mazabu har zuwa na kasa har sai abin da hali ya yi.

Sanarwar hakan na kunshe ne a cikin wata wasika da kwamitin riko na jam’iyyar ya aikewa da Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC).

Wasikar, mai dauke da kwanan watan shida ga watan Yulin 2021 na dauke ne da sa hannun shugaban rikon kwarya na jam’iyyar, Gwamna Mai Mala Buni da Sakatarenta, Sanata John James Akpanudoedehe.

A cewar wasikar, “Muna so mu sanar da wannan hukumar cewa jam’iyyarmu ta dage manyan tarukanta a dukkan matakai har zuwa wani lokaci da zamu sanar a nan gaba.

“Wannan na matsayin ankararwa ce a hukumance, kamar yadda sashe na 85 na Dokar Zabe ta Kasa ta Shekarar 2010 da aka yi wa kwaskwarima ya tanada.

“Yayin da muke fatan samun cikakken hadin kanku, muna mika cikakkiyar godiya,” inji APC a cikin wasikar.

To sai dai a wata sanarwa da Sakataren jam’iyyar na riko, Sanata John ya fitar a Abuja ranar Asabar, ya ce wasikar da ake ta yamadidi da ita ba ta nufin cewa sun dage tarukan.

 

“Yadda har wasikar ta fita daga INEC shine ma babban abin mamaki. Mun yi hakan ne don tabbatar da bukatar sashe na 85 na dokar zabe da ya tanadi sanar da hukumar akalla kwanaki 21 kafin lokacin, kasancewar ranar da muka ba su ba wai babu canji ba ne a cikinta,” inji sanarwar.

 

Kamar yadda yake a jadawalin jam’iyyar na farko dai wanda Daraktan Tsare-tsarenta, Farfesa Al-Mustapha Ussiju Medane ya fitar, za a fara shirye-shiryen tarukan ne da sayar da fom din takara a matakin mazabu daga ranar daya ga watan Yuli sannan a kammala ranar bakwai ga wata.