Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta sake dage ranar gudanar da babban taronta na kasa har sai abin da hali ya yi.
Wannan dai na zuwa ne a sakamakon rikicin cikin gida da jam’iyyar take fuskanta a wasu sassanta bayan ta tsayar da ranar 26 ga watan Fabrairu tun da farko.
- ‘’Yan bindiga sun yi wa daliban da suka sace ciki’
- Yadda angon ’yan mata 8 ke rayuwa cikin annashuwa
Jam’iyyar APC ta sanar da dage taronta a cikin wata takarda da ta aika wa Hukumar Zabe ta Kasa INEC mai dauke da sa hannun shugabanta na riko, Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe.
“Muna sanar da Hukumar Zabe cewa jam’iyyarmu ta yanke shawarar gudanar da zaben shiyoyi a ranar Asabar 26 ga watan Maris.”
Haka kuma, sanarwar jam’iyyar APC ta fitar ta ce ta dogara ga sashe na 85 na Dokar Zabe ta shekarar 2010 da aka yi wa gyaran fuska da kuma bin sashe na 12 sakin layi na 6 na Kundin Tsarin Mulkin jam’iyyar ta APC.
Ya zuwa yanzu dai jam’iyyar ba ta sanya ranar gudanar da babban taronta na kasa ba.
Sai dai wasu majiyoyi daga Babban Ofishin Jam’iyyar sun shaida wa Aminiya cewa a watan Maris din ake sa ran gudanar da babban taron.