Dan takarar Jam’iyyar APC, Lawan Pagu ya lashe zaben cike gurbi da aka gudanar a mazabar Chibok ta Jihar Borno ranar Asabar.
Baturen zaben, Farfesa Baba Shehu Waziri, ya bayyana Lawan Pagu a matsayin wanda ya lashe zaben bayan kammala kirga kuri’u a cibiyar tattara sakamakon zaben da ke garin Chibok.
Waziri ya ce dan takarar APC ya samu kuri’u 9,101 inda ya doke babb6 abokin hamayyarsa, Habila Bello na Jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 2,117.
“Lawan Pagu na Jam’iyyar APC ya yi nasarar lashe zaben kuma ya cika duk ka’idojin da suka kamata,” in ji shi.
- An yi garkuwa da ’yan daukar amarya 55 a Katsina
- Kotu ta ɗaure Farfesan Jami’ar Maiduguri shekaru biyu
Daga cikin kuri’u 11,427 da aka kada, ya ce dan takarar ADC Abdullahi Gamboru ya samu kuri’u 69; Hamid Zamzam Abbas na APP kuri’u 63, Abdullahi Lawan Talba na APM 48, Haruna Shettima na APP 17 sai Maina Sheriff na SDP kuri’u 12.
An gudanar da zaben cike gurbi na majalisar dokokin Chibok ne sakamakon rasuwar Hon. Nuhu Clerk, wanda ya rasu jim kadan bayan ya lashe zaben a karkashin inuwar APC a babban zaben 2023 da ya gabata.